Hajj 2021: Duk wanda ba a yi wa rigakafin korona ba ba zai yi ibadar ba – Saudiyya

Masu gudanar da aikin Hajji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan ƙasashen waje ba su gudanar da aikin Hajji a shekarar 2020 ba saboda annobar korona

Ma'aikatar Lafiya ta Saudiyya ta sharɗanta wa dukkan alhazai daga ƙasashen waje su yi allurar rigakafin cutar korona sau biyu kafin gudanar da aikin Hajjin shekara ta 2021.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito ma'aikatar na cewa wajibi ne a yi wa mahajjaci allura ta biyun, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince da ita. mako ɗaya kafin ya isa Saudiyya,

Kazalika, alhazai za su je da takardar gwajin cutar wadda ke nuna cewa ba sa ɗauke da ita wadda kuma aka yi kwana uku kafin isarsu ƙasar.

Haka nan sai sun killace kansu na tsawon kwana uku. Alhazai za su fito ne kawai bayan gwaji ya tabbatar ba sa ɗauke da cutar.

Ma'aiikatar ta kuma ƙayyade cewa 'yan shekara 18 zuwa 60 ne kaɗai za su yi aikin hajji na shekarar Hijira ta 1442.

Sauran sharuɗɗan sun haɗa da rataya alama a wuya da bayar da tazarar aƙalla mita ɗaya da rabi tsakanin alhazai. Sannan kuma rukunin mutum 100 ne za su riƙa gudanar da ayyukan ibada a lokaci guda.

Ga mazauna Saudiyya kuwa, ma'aikatar lafiyar ƙasar ta ce tana sa ran yi wa kashi 60 cikin 100 na mazauna biranen Makka da Madina rigakafin korona kafin 1 ga watan Zul Hijja - watan aikin Hajji - a cewar rahoton Okaz.

Daga cikin ƙa'idojin da aka shimfiɗa musu, wajibi ne duk ma'aikan Hajji sai sun yi rigakafin, wadda ƙasar ta amince da ita, sau biyu.

Su ma alhazai mazauna Saudiyya dole ne a yi musu allurar sau biyu kafin 1 ga watan na Zul Hijjah.

Annobar korona ta sa Saudiyya ta hana alhazai daga ƙasashen waje shiga ƙasar domin gudanar da aikin Hajji na 2020, inda mutum kusan 1,000 ne kacal suka gudanar da ibadar.