Masu zabe na tururuwa domin kada kuri'a a Kongo bayan tababa

Guy-Brice Parfait Kolelas a lokacin zaben 2016

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Guy-Brice Parfait Kolelas ya zo na biyu a zaben shugaban kasar ta Jamhuriyar Kongo na 2016

Masu zabe na tururuwa a Jamhuriyar Kongo domin kada kuri'a a zaben shugaban kasar da ake ganin shugaba mai karfin iko Denis Sassou Nguessou zai yi tazarce.

Shugaba mai-ci Denis Sassou ya shafe shekara 36 a kan mulki.

Yana fuskantar abokan takara shida, amma babban abokin hamayyarsa, Guy-Brice Parfait Kolelas, na kwance a asibiti bayan da ya kamu da cutar korona a ranar Juma'a.

Babbar gamayyar 'yan hamayya ta kasar ta kaurace wa zaben shugaban kasar, wadda ke da dimbin arzikin mai. Shuwagabannin addini da masu raji kare hakkin dan adam na nuna shakku kan tabbatr da gaskiya a zaben.

Idan ba a samu wanda ya yi nasara ba kai tsaye, za a je zagaye na biyu.

Bayan zaben shekara ta 2016 an daure 'yan takara biyu da suka kalubalanci Shugaba Nguessou a zaben shekara ashirin

Rashin lafiyar dan takarar na hamayya, Guy-Brice Parfait Kolelas, bayan da ya kamu da cutar ta Korona, ya sa aka yi tababa kan gudanar da zaben shugaban kasar kamar yadda aka tsara, ran Lahadin.

Tsarin mulkin kasar ya bayar da damar jinkirta zabe idan wani dan takara ya mutu ko kuma ba zai iya shiga zaben ba saboda wata larura.

Mr Kolelas, wanda ya kasance daya daga cikin 'yan takara bakwai a zaben kasar ta Dumokuradiyyar Kongo, shi ne fitacce kuma jigo a bangaren 'yan hamayya da ke kalubalantar Shugaba Denis Sassou Nguessou, wanda ke kan mulki tsawon shekara talatin da bakwai kuma da dama na ganin shi ne dai zai sake cin zaben.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Tun 1979 Shugaba Denis Sassou Nguesso yake kan mulki, in banda shekara biyar da ya sarara

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Shugaban kwammitin yakin neman zaben dan takarar na hamayya ya tabbatar da sahihancin wani hoton bidiyo da ake yadawa a shafukan intanet da ke nuna Mista Kolelas mai shekara sittin da daya, kwance a galabaice a gadon asibiti.

A hoton bidiyon ana ganin Mista Kolelas sanye da na'urar taimaka masa da iskar shaka, wadda ya dan cire na dan lokaci a da kyar da kyar yana gaya wa magoya bayansa cewa yana cikin mawuyacin hali na sai yadda ta kasance.

Sai dai duk da haka ya bukaci magoya bayan nasa da su fita su yi zaben domin domin tabbatar da canji.

Mista Kolelas, wanda daman yana da cutar sukari, ya kamu da cutar korona inda ya ce yana cikin wani mawuyacin hali na neman tsira da ransa.

Iyalansa sun ce suna kokarin ganin yadda za a dauke shi daga asibitin da yake na 'yan kasuwa a babban birnin kasar, Brazzaville, zuwa Faransa domin yi masa magani.

Mista Kolelas ne ya zo na biyu, da kusan kashi goma sha biyar cikin dari na kuri'un da aka kada, bayan Sassou N'Guesso a zaben shugaban kasar na 2016.

A kwanakin nan dan hamayyar ya rika caccaka da sukar shugaba mai ci, har yana cewa Jamhuriyar Kongo ta zama kasa ta mulkin kama-karya da danniya.

Dennis Sassou N'Guesso ya kasance shugaba na uku a nahiyar Afirka da ya dade a kan mulki, inda ya kama mulkin kasar daga 1979 zuwa 1992, sannan kuma ya kara kama iko tun daga 1997 har zuwa yau a kasar da katafariyar makwabciyarta Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo ta sa ba a jin duriyarta sosai.