Kotu ta yanke wa wadanda suka yi fyade hukuncin kisa

Kotun ta yi zama cikin tsattsauran matakan tsaro

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

An tsaurara matakan tsaro a kotun da ke lardin Lahore yayin yanke hukuncin

Wata kotun musamman a birnin Lahore na Pakistan ta yanke wa wasu mutane biyu hukuncin kisa, kan laifin fyade na gungu, wanda ya harzuka jama'a a shekarar da ta wuce, ya kuma haddasa gagarumar zanga-zanga ta mata a kan cin zarafin da ake yi musu na lalata

A watan Satumba na shekarar da ta gabata ne dai mutanen biyu Abid Mehli da Shafqat Ali suka yi wannan aikta-aikata, a lokacin da matar wadda hukumomi ba su bayyana ta ba tana tafiya a motarta cikin dare tare da 'ya'yanta 'yan kanana biyu, mai ya kare mata a motar, inda ta yi waya domin samun taimako.

a lokacin da take zaman jira ne sai kwatsam wadannan kattai 'yan shekara 30 da doriya, suka far ma ta, suka balla motar suka fitar da ita da 'ya'yan zuwa wani daji a kusa suka yi mata fyade, tare da kwace mata kudi da kayan kawa da take sanye da su, suka kuma tsere.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dubban jama'a a fadin Pakistan sun shiga zanga-zangar neman yin adalci da kare hakkin mata a shekarar da ta wuce

Lamarin ya harzuka jama'a a biranen kasar ta Pakistan aka yi ta zanga-zanga, musamman ma kan kalaman da wani babban jami'in 'yan sanda ya yi cewa matar ce da laifi kan abin da ya faru;

da cewa a wane dalili ne za ta yi wannan tafiya a wannan hanya da tsakar dare, kuma ba tare da isasshen mai a motar ba.

A rahoton binciken da 'yan sanda suka gudanar, sun ce harin ya sa matar ta kadu, sosai, amma kuma duk haka ta iya ba su bayanai masu muhimmanci kan wadanda suka yi mata ta'annatin, har aka kai ga kamasu.

Bayan da mutanen suka shiga hannu, kotu ta musamman da ta yi musu sharia ta same su da laifin fyade na gungu da satar mutane da fashi da makami da kuma sauran laifuka na ta'addanci.

Sai dai lauyan da ya tsaya musu ya ce za su daukaka kara a kan hukuncin kisan da aka yanke musu.

A watan Disamba ne hukumomin kasar ta Pakistan suka amince da sabbin dokki na fyade, da ke tabbatar da ganin ana yin shari'a cikin hanzari ba da wani bata lokaci ba, da kuma yin hukunci mai tsanani.