Nowruz: Yadda Farisawa a sassan duniya ke bikin sabuwar shekararsu

Two Iranian medical personnel wearing protective suits pose for a photograph as they stand next to a Haft-Seen (Seven-S) table, The historical symbol for the Iranian New Year, in a COVID-19 ward in Firoozabadi hospital in Shahr-e-Rey neighborhood in the south of Tehran on the day of Nowruz

Asalin hoton, Getty Images

Miliyoyin mutane a faɗin duniya sun yi bikin Nowruz - bikin murnar sabuwar shekarar Farisawa da kuma murnar shiga lokacin bazara.

Nowruz yana farawa ne daga lokacin bazara, lokacin da yini da dare suka kasance daidai.

Ana gudanar da bikin sabuwar shekarar ne galibi a Iran da Afghanistan da yankunan Kurdawa na Iraƙi da Turkiya da Indiya da wasu mazauna ƙasashen waje a sassan duniya.

Wannan shekarar - a kalandar Farisa ita ce ta 1400 - an gudanar da biki a wurare da dama duk da dokokin taƙaita yaɗuwar korona.

A wani dogon ɗakin asibitin Firoozabadi a Tehran, jami'an lafiya sun yi bikin ne tare da majinyata, inda suka ƙawata teburi da kayan abinci.

Jami'an kiwon lafiya a Tehran sun gudanar da bikin Nowruz tare da majinyatan korona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jami'an kiwon lafiya a Tehran sun gudanar da bikin Nowruz tare da majinyatan korona

A dandalin Tajrish, ɗaya daga cikin wuri mafi cunkosu a Tehran, mutane suna sayen abinci da sauran kayayyaki daga kasuwa.

Kayan abinci da aka jera domin masu ɓukata albarkacin sabuwar shekara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kayan abinci da aka jera domin masu ɓukata albarkacin sabuwar shekara

Bisa al'ada a Iran, mutane suna yi wa teburin Nowruz ado da wasu abubuwa - kamar kifi, ganyen alkama, kyandir da madubai.

Ana amfani da Kifi mai launin ruwan zinari wajen ƙawata bikin Nowruz

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana amfani da Kifi mai launin ruwan zinari wajen ƙawata bikin Nowruz

A Turkiya, dubban Ƙurdawa ne suke cashewa da kaɗe-kaɗe da rawa a Santanbul.

Dubban Ƙurdawa na gudanar da bikin a Turkiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubban Ƙurdawa na gudanar da bikin a Turkiya
Ana kaɗe-kaɗe da raye-raye a wurin bikin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana kaɗe-kaɗe da raye-raye a wurin bikin

Farisawan Indiya suna zuwa wurin ibadarsu a ranar bikin sabuwar shekarar. A nan, wani uba ne tare da ɗansa kan hanyarsu da zuwa wurin ibada a Tardeo da ke Mumbai.

Wani uba a wurin ibadar ƴan farisa a Mumbai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani uba a wurin ibadar ƴan farisa a Mumbai

A Srinagar, yankin Kashmir da ke ƙarƙashin Indiya, suna gudanar da al'adu a bikin Nowruz duk shekara, inda ake amfani da wasu halittu da ke shan jinin mutanen da ke neman maganin wata matsala ta lafiya.

Ana gudanar da maganin ne a wani tafki da ake kira Dal Lake a Srinagar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana gudanar da maganin ne a wani tafki da ake kira Dal Lake a Srinagar

Bayan faɗuwar rana musamman a garin Akra yankin Ƙurdawa na Iraƙi, mutane suna gudanar da wasan wuta.

Iraqi Kurdish people carry fire torches, as they celebrate Nowruz Day, a festival marking the first day of spring and the new year, amid the spread of the coronavirus disease (COVID-19), in the town of Akra near Duhok, in Iraqi Kurdistan

Asalin hoton, Reuters

Fire torches are seen as Iraqi Kurdish people celebrate Nowruz Day, a festival marking the first day of spring and the new year, amid the spread of the coronavirus disease (COVID-19), in the town of Akra near Duhok, in Iraqi Kurdistan

Asalin hoton, Reuters

Dukkanin hotunan suna da haƙƙin mallaka.