Masu sa dokar kulle kan korona 'yan kama-karya ne - Bolsonaro

Shugaba Jair Bolsonaro

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaba Bolsonaro na Brazil na shan suka kan yadda bai dauki lamarin cutar korona da muhimmanci ba

Shugaban Brazil, Jair Bolsonaro, ya bayyana gwamnonin jihohi da shugabannin biranen kasar da ke sanya dokoki da matakan kulle don yaki da annobar korona ta karo na biyu a matsayin 'yan kama-karya.

Mr Bolsonaro ya ce gwamnatinsa ta yi duk abin da za ta iya a kan annobar ta korona, a don haka yanzu lokaci ne da za a sake bude harkokin kasuwanci da tattalin arziki.

Shugaban yana jawabi ne ga daruruwan magoya bayansa da suka taru a kofar fadar gwamati a Brasilia domin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Ya ce, '' ku san abu daya shi ne, cewa ina samun kwarin guiwata ne daga ni kaina da kuma ku. Saboda haka idan wani yana tunanin cewa wata rana za ta zo da za mu sallama 'yancinmu to fa ya yi kuskure......''

Tun farkon bayyanar annobar ta korona, shugaban na Brazil ya yi watsi da irin kalamai da rahotannin da gargadin da ake yi a kan illar cutar.

Sashen bayar da kulawar gaggawa na asibitocin Brazil na kara cika da masu fama da cutar ta korona

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Sashen bayar da kulawar gaggawa na asibitocin Brazil na kara cika da masu fama da cutar ta korona

Shugaban ya jinkirta sayen allurar rigakafin cutar, har ma kuma a baya bayan nan ya yi kira ga jama'a da su daina damuwa da fargaba da koke a kan cutar ta korona.

Sai dai abin da ke ba wasu 'yan kasar ta Brazil mamaki da tayar musu da hankali, shi ne Shugaba Bolsonaro na yin kalaman nasa na baya bayan nan ne a lokacin da cutar ta fi tsanani a kasar.

Lokacin da asibitoci ke cika da marassa lafiya, kuma yawan masu kamuwa da cutar da kuma wadanda take hallakawa ke ci gaba da karuwa.

Sama da mutane dubu biyu da dari biyu ne aka yi kiyasi akalla na mutuwa a sakamakon kamuwa da cutar a Brazil din a duk rana