Ambaliyar ruwa a Australia: Hotunan mummunar ambaliyar ruwa mafi girma cikin shekara 50

Ambaliyar ta mamaye Raymond Terrace

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mazauna yankin na kallon yadda ruwan ya mamaye titunan yankin Raymond Terrace

Ambaliyar ruwan da aka dade ba a ga irinta ba cikin gwamman shekaru ta mamaye New South Wales, yayin da ake ci gaba da tafka ruwa kamar da bakin kwarya musamman a yankunan gabar teku na kasar Australia.

Tuni aka kwashe kusan mutane 18,000, saboda tumbatsar koguna da madatsun ruwan da ke babban birnin kasar Sydney da wasu yankunan da ke kusa da gabar teku.

Jami'ai sun ce za a ci gaba da fuskantar matsalar nan da makwanni masu zuwa, tare da bukatar mazauna yankunan su yi takatsantsan.

Rahotanni sun tabbatar da mummunar barna da ambaliyar ta haddasa.

Wasu sabbin ma'aurata sun ce a kan idanunsu ambaliyar ta share gidansu, a ranar da ya kamata ta zamo ta amarcinsu.

mota ta kusa nutsewa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wannan motar ta kusan nutsewa a cikin ruwan arewa maso gabashin Sydney
Allon wuraren da ambaliyar ta shafa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ambaliyar da kogin Nepean ya yi ta mamaye wurin shakatawar da ke yankin Penrith
An dauki hoton mace da jariri a cikin ruwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ita ce mummunar ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru 50, an dauki hoton wannan matar a cikin ruwan da ya tumbatsa daga kogin Hawkesbury da ke Sydney
Gida da zabtarewar kasa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Zabtarewar kasa ta kusa ruguje gidan nan, hakan ya tilasta rufe hanya a Newcastle
Kogin Parramatta ya yi ambaliya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Makwabtan yankin na kallon yadda ruwan ke ambaliya daga kogin Parramatta a Sydney
Boys slide in mud in New South Wales

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wasu yara sun zabi yin wasannin zamiya a lokacin da ake ambaliyar a wurin shakatawa na Sarki Edward da ke Newcastle