Rikicin Makiyaya: Abdullahi Adamu ya ce ana fakewa da makiyaya domin raba kan 'yan arewa

Abdullahi Adamu

Asalin hoton, Abdullahi Adamu

Daya daga cikin dattawan arewacin Najeriya kana ɗan majalisar dattawa daga jihar Nassarawa Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ana ƙoƙarin fakewa da sunan hare haren da ake zargin makiyaya na kaiwa wasu jihohin ƙasar domin raba kan al'ummar yankin.

Yayin wata hira da BBC Sanata Abdullahi Adamu, ya ce rikicin makiyaya ya samo asali ne sakamakon cinye hanyoyi ko burtalan da suke bi, da kuma dazukan da aka keɓe musamman don kiwo, sannan aka ƙi samar da wani shiri don ganin sun gudanar da harkokinsu.

''Ana neman dalili ne domin bata sunan makiyayi don a la'ance su, ana maganar kiwo wake maganar kudu ?, ai kowa ya san kiwo a arewa yake, don haka wuta ce ake kunnowa domin ganin an raba kan a;'ummar arewa'' a cewar Sanatan.

Ya ƙara da cewar matsawar ana son kawo ƙarshen wannan matsala, to kuwa dole ne gwamnati ta fahimci haɗarin da ke tattare da bari a rika yin kiwo barkatai, alabashi idan ta fahimci haka sai ta samarwa makiyayan wata hanya da za su rika gudanar da harkokinsu.

A cewarsa ''Dole mu so juna, mutumin kudu ai bai san wata ƙabila Hausa Fulani ba, a ganinsa duk a dunƙule muke, wannan bai isa ba, yanzu kuma so ake a raba kan Hausa da Fulanin ma''.

A halin da ake ciki dai matsalar tsaro na ƙara ƙamari a Najeriya baki ɗaya, musamman ma arewacin ƙasar, inda ake samun hare hare kusan kullum a wasu jihohi, inda 'yan bindiga ke kashe mutane sannan su yi garkuwa da wasu domin neman kudin fansa.

Ana danganta masu kai irin waɗanan hare hare da makiyaya dake zaune a dazuka.

Wannan matsala ta yi ƙarami ne a lokacin gwamnatin Shugaba Buhari inda aka yi garkuwa daruruwan mutane yayin da aka kashe da dama.

Wani abu da ya kara fito da matsalar ga idon duniya shi ne yadda yan bindigar ke sace dalibai a makarantu, abin da masu sharhi ke ganin zai iya kawo gagarumin koma baya ta fuskar samar da ilimi a yankin.