Turai za ta tsaurara matakan samar da riga-kafin korona

Rigakafin AstraZeneca

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Hukumar magunguna ta Turai ta kawar da fargabar da ta sa wasu kasashe dakatar da amfani da rigakafin AstraZeneca

Hukumar Tarayyar Turai za ta fitar da wasu bayanai kan tsauraran matakan da za ta dauka game da samar da allurar rigakafin korona a kasashe, yayin da hukumar ke sa-in-sa da kamfanin AstraZeneca.

Hukumar ta Turai ta zargi kamfanin da saba yarjejeniyar da suka kulla da shi, wajen gaza samar da yawan allurar rigakafin da gibin miliyoyin kwalabe kamar yadda ya yi alkawari.

Kasashen Turai na fama da samun karuwar mutanen da ke harbuwa da cutar, sannan kuma mutane na dari-dari da rigakafin AstraZeneca da aka yi a Birtaniya, bayan da wasu kasashe da dama suka dakatar da amfani da rigakafin na wani lokaci.

Matakin ya biyo bayan fargabar da ake yi game da shi, abin da daga bisani hukumar kula da magunguna ta Turai ta yi watsi da illar da ake magana a kai.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Italiya na daga kasashen da suka dakatar da amfani da rigakafin AstraZeneca kafin a musanta fargabar da ake yi a kansa

A ranar Larabar nan ne shugabannin kasashen Turai za su duba tsarin baya bayan nan na samar da rigakafin na hukumar kasashen kungiyar ta EU.

Kungiyar ta Turai ta ce abu ne da ba za ta lamunta ba ganin cewa ta yi odar sama da kwalaben rigakafin miliyan 40 a watanni biyu da suka gabata, ciki har da miliyan goma da Birtaniya ta yi, amma a ce abin da ta samu kusan bai taka kara ya karya ba.

Wasu majiyoyi na kusa da hukumar ta Turai sun ce, matakan da za ta bayyana ba wai za ta sanar da hana fitar da maganin ba ne, illa dai za ta bayyana yadda za ta tabbatar kasashen nata na samun rigakafin yadda ya kamata kuma a kai a kai ba yankewa.

Ana ganin shirin zai kunshi yadda hukumar za ta tabbatar da ganin cewa duk rigakafin da za a fitar zuwa wata kasa daga Turan dole ne ya kasance a bisa wasu ka'idoji muhimmai.

Ka'idojin da suka hada da yawan yadda ake rigakafin a kasar da za a kai maganin, da kuma yawan allurar rigakafin da ita kanta kasar take fitarwa.

Sannan kuma jami'an hukumar za su rika dubawa su ga yadda kamfanin da ke samar da rigakafin ke cika alkawarin da ya yi kan samar da rigakafin ga kasashen Turai, kuma a kan lokaci.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Annobar korona ta haifar da illa ga tsarin kula da lafiya da sauran fannoni a duniya

Babban tasirin da ake ganin wannan zai yi ga Birtaniya shi ne, idan aka hana shigar da rigakafin kamfanin Pfizer da ake yi a Belgium, a karkashin sabuwar yarjejeniyar da ke tsakaninsu, to amma jami'ai na kawar da yuwuwar yin hakan.

Wasu majiyoyi na Biraniya sun jaddada cewa tuni kasar ta aika da muhimman ababan da ake bukata na hada rigakafin na kamfanin Pfizer zuwa ga kungiyar ta EU.

Sannan kuma suka ce Birtaniyar ta taka muhimmiyar rawa wajen zuba jarin samar da rigakafin tun da farko.