Coronavirus: An yi wa ‘yan Najeriya fiye da dubu 250 allurar riga-kafin korona

rigakafin korona

Asalin hoton, EPA

Gwamnatin Najeriya ta ce ya zuwa yanzu an yi wa 'yan kasar fiye da 250,000 allurar riga-kafin cutar korona.

Wasu alkaluma da Hukumar Lafiya a tamakin farko ta kasar ta fitar sun nuna cewa ya zuwa ranar 23 ga watan Maris, an yi wa mutum 215,277 allurar riga-kafin korona.

Alkaluman sun nuna cewa jihar Lagos ce a sahun gaba a yawan wadanda aka yi wa riga-kafin, inda aka yi wa mutum 58,461, kamar dai yadda ita ce ta fi kowacce jiha yawan wadanda suka kamu da cutar korona tun bayan bullarta a Najeriyar a bara.

Idan muka je arewacin kasar kuwa, jihar Bauchi ce kan gaba, an kuma yi wa mutum 23,827 allurar riga-kafin ta AstraZeneca.

Jihar Jigawa ke biye mata da mutum 20,800.

Sauran jihohin da aka yi riga-kafin sun hada da:

 • Adamawa 7,407
 • Akwa Ibom 127
 • Anambra 132
 • Bayelsa 552
 • Binuwai 146
 • Borno 653
 • Cross River 948
 • Delta 915
 • Ebonyi 77
 • Edo 2,645
 • Ekiti 1,049
 • Enugu 956
 • Abuja 8,616
 • Gombe 203
 • Imo 1,908
 • Kaduna 14,572
 • Kano 3,903
 • Katsina 10,002
 • Kwara 12,016
 • Nasarawa 6,801
 • Ogun 19,257
 • Ondo 4,205
 • Osun 6,658
 • Filato 883
 • Rivers 1,951
 • Sokoto 98
 • Yobe 5,509

Sai kuma jihohin da ba a yi wa ko mutum guda rigakafin cutar korona ba, sun hada da:

 • Abia 0
 • Zamfara 0
 • Kebbi 0
 • Niger 0
 • Kogi 0
 • Taraba 0
 • Oyo 0