An yi muhawara a Tuwita kan ko Naira ta rage daraja ne ko kuma ba ta da amfani

naira

Asalin hoton, Getty Images

Ƴan Najeriya sun wayi gari ranar Laraba suna tafka muhawara a shafin sada zumunta na Twitter kan yada kuɗin da suke kashewa na Naira ke rage daraja.

Da dama dai tambayar da suke da bayyana ra'ayoyi a kai ita ce shin kuɗin naira rage daraja kawai yake yi ko kuma ba shi da amfani kwata-kwata.

Babu mamaki wannan muhawara ta biyo bayan karyewar da ake ci gaba da gani na darajar kuɗin a kasuwanni, musamman a watanin baya-bayan nan inda naira take kai wa 480 zuwa 500 a kan dala guda ta Amurka.

Hukumomin Najeriya dai na cewa suna sake rage darajar naira ce domin cike gibin da ake fama da shi a fannin tattalin arziki.

Sannan shi ma Asusun Lamuni Na Duniya IMF a watannin baya ya shawarci mahukuntan ƙasar kan alfanun da rage darajar kuɗin ga bunkasar tattalin arzikinta.

Sai dai a duk lokacin da darajar naira ta yi ƙasa ana samun hauhawar farashi, kuma rayuwa na ƙara tsada matuka.

Galibin ƴan kasuwa na amfani da wannan damar wajen kare hujojjinsu a ƙari ko tsadar kayayyaki.

Me ƴan Najeriya ke cewa?

To kusan dai galibi kowa tambaya yake jefa wa da kuma kwatanta kuɗin naira da sauran kuɗaɗen da ake kashewa a harkokin kasuwanci a Najeriya, misali dalar Amurka ko fam na Ingila.

Akwai kuma masu ra'ayin cewa bai kamata ake kwatanta naira da kuɗin ƙetare ba, la'akari ko auna abin da za ka iya saye da kuɗin ya kamata a rinƙa magana a kai.

Wale Adetona na da ra'ayin cewa: A shekarun baya Naira 150,000 daidai take da dala dubu ɗaya, amma a yanzu Naira 150,000 z tai ba ka dala 312 ne kawai. Ku yi tunani a kai.

@DrOlufunmilayo ya ce: A 2001: $1 na kan naira 113, A 2002: $1 na kan naira 126, A 2010: $1 na kan naira 149, A 2011: $1 na kan naira 156, A 2015: $1 na kan naira 197, A 2016: $1 na kan naira 305, A 2017: $1 na kan naira 306, Amma a yau 2021: $1 na kan naira 486. Ina fatan ba za mu shaida ranar da naira za ta tashi tamkar takarda ba.

Sai dai wasu daga cikin masu muhawarar ra'ayinsu ya bambanta:

@_SirWilliam_ ya ce: Ba abu ne mai muhimmanci ba a zauna kwatanta ko naira na da rauni ko ba ta da amfani. Ba a gina tattalin arziƙi kan surutan baka. Naira na iya daraja ne kaɗai ta daukar matakan da suka dace domin cimma daidaituwa.

Tasirin ƙaruwar darajar Naira

Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashe masu tasowa da suke ƙayyade darajar kudinsu, inda take tsara yadda dala za ta shiga ta fita daga ƙasar da kuma ajiyar kuɗin CBN.

Masana tattalin arziki dai sun jima suna tsokaci cewa faɗuwar darajar dala za ta yi amfani ga talakawa da kuma gwamnatin ƙasar.

Ana ganin idan farashin kayayyakin ƙasar waje ya sauka ko ya hau sai ya shafi mutane da kuma abubuwan da suke sarrafawa a cikin gida.

Kazalika akwai yiwuwar Nairar ta gaza riƙe darajar tata matuƙar CBN ya dakatar da bayar da kuɗaɗen waje ga ƴan kasuwa.