Ƴan adawa ke yaɗa jita-jitar ɓaraka tsakanin Buhari da Tinubu - Fadar Shugaban Ƙasa

Buhari da Tinubu

Asalin hoton, Presidency Twitter

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce babu wata ɓaraka da ke tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da babban na hannun damarsa a siyasance kuma jagoran jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Fadar shugaban ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaba Buhari kan yada labarai Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari da Asiwaju dukkansu sun duƙufa wajen gina jam'iyyar APC da samar da sauyi, kuma wannan alƙawari ne da suka ɗaukar wa ƴan Najeriya.

A baya-bayan nan dai ana ta yaɗa rahotanni kan cewa ɓaraka ta kunno kai tsakanin mutanen biyu, sai dai Garba Shehu ya ce rahotannin ƙarya ne kuma "aikin wasu masu haɗa tuggu ne a shafukan sada zumunta.

"Abin kunya ne a ce wasu ɓangarori na yaɗa labarai na dogara kan ƙirƙirar ce-ce ku-ce, da ke samar da gungun masu suka waɗanda ke aiki ta bayan fage wajen assasa irin labaran nan da suke zallar ƙarya ce.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati na sane da duk masu mugun fata da ƴan gaza gani da ke yaɗa labaran ƙanzon kurege ga mutane, kan dangantakar shugabanninta da kuma son ganin bayan jam'iyyar.

"Babu shakka shugaban ƙasa da jam'iyyarsa na mayar da hankali ne kan ci gaba da zaman lafiya da tsaro da sake fasalin tattalin arziki da kuma yaƙi da cin hanci a ƙasar, kuma babu abin da zai ɗauke musu hankali daga hakan.

"Ƙoƙarin ruɗa mutane ba zai yi nasara ba," a cewar Garba Shehu.

Kazalika sanarwar ta ce Bola Tinubu na daga cikin jagororin siyasar da Shugaba Buhari yake matuƙar ganin ƙimarsu a ƙasar, saboda tsayuwarsa a kan manufofinsa komai tsanani.

A cewar sanarwar, Tinubu na daga cikin jigon samar da jam'iyyar APC da ci gabanta sannan ƙawancen kullum ƙara ƙarfi yake yi.

Ta kuma ce rashin ganin Tinubu akai-akai a Fadar Shugaban Ƙasa ba ya nufin cewa sun ɓata sai dai don cewa shi ɗin ba ya daga cikin mambobin majalisar zartarwar gwamnatin.

"Batun cewa ba a ganinsa a Villa kullum ba shi zai sa abotarsu da shugaban ƙasa ko da wannan gwamnatin ta yi rauni ba."

A ina batun jita-jitar ta samo asali?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tun a watan Fabrairun da ya gabata wani sabon rikici ya fara kunno kai a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, sakamakon wasu kalamai da aka ji sun fito daga bakin babban jigon nata Bola Ahmed Tinubu, kan batun sabunta rijistar ƴaƴan jam'iyyar.

Wataƙila jita-jitar da ake yaɗa wa a yanzun kan ɓaraka tsakanin shugabannin biyu ba za ta rasa nasaba da wannan batun ba.

Shi dai Tinubu wanda ake kyautata zaton zai nemi tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya ce aikin sabunta rijistar ƴaƴan jam'iyyar a jihohin ƙasar baki ɗaya ba shi da wani tasiri.

"Sabunta rijistar da jam'iyyar ke yi tamkar a sanya ɗaya ne kana kuma a cire ɗaya, don haka ni ina ganin ba wata ƙaruwa ba ce'', a cewar Tinubu.

Wannan kalamin ya sa wasu ƴaƴan jam'iyyar na cewa da walakin goro a miya, kuma alama ce da ke nuna cewa bai ji daɗin abin da ake yi ba, saboda a cewarsu, aikin rijistar zai iya rage masa ƙarfin mamayar da ya yi wa jam'iyyar, da kuma tasirin da yake da shi a cikinta.

Sai dai wasu makusantan Bola Tinubun sun cewa ba a fahimce shi ba ne, kuma babu yadda sabuwar rijistar za ta shafi ƙarfin fada ajin da yake da shi a jam'iyyar.