Ikirarin APC na son shafe shekara 32 tana mulkar Najeriya ya janyo ce-ce-ku-ce

NIG PDP

Asalin hoton, Getty Images

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya da sauran jama'ar ƙasar na ci gaba da mayar da martani game da furucin da jam`iyyar APC mai mulki ta yi cewa za ta so ta shafe akalla wa'adi tara tana mulkin kasar domin a ci gajiyarta yadda ya kamata.

Furucin na jam'iyyar APCn da ya janyo cece-kuce ya fito ne daga bakin Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban riko na jam'iyyar, mai Mala Buni lokacin da yake kaddamar da kwamitin tuntubar jam'iyyar.

A cewarsa, samun wannan dama zai bai wa APC ikon dorawa kan ayyukanta na bunkasa rayuwar al'ummar Najeriya.

Sai dai PDP ta bayyana wannan furucin a matsayin magaganin barci kawai. Sanata Umar Ibrahim Tsauri, Sakataren Jam'iyyar PDP ya ce ita ma PDP ta yi irin wannan burin na shafe shekara 60 tana mulki.

"Maganar wani ya tashi ya ce zai yi mulki har zuwa lokaci kaza, toh yana son ya je gaban Allah ne musamman mulki irin wanda APC ke yi wa yan Najeriya, mu mun sani dukkan mutum wanda yake da rai da hankalin kansa, ba zai zabi APC ba a 2023 balle har a ce ta kara yawan wa'adi na wasu lokuta". in ji Sanata Tsauri.

Hangen Masana kan kalaman APC

Wannan batu dai ya haifar da takaddama inda masana siyasa ke ganin kalaman na iya tada kura kuma tana iya fuskantar turjiya wajen yan Najeriya.

A cewar Dakta Abubakar Kyari, malami a jami'ar Abuja ya bayyana cewa wasu suna iya kallon lamarin a matsayin kokarin APC na son yin kane-kane ko ma ta tabbata a kan karagar mulki - abin da ya ce karen tsaye ne ga tsarin dimokradiyya.

"Irin dimokradiyyar da muke yi a kan yi zabuka kowane bayan shekara hudu kuma ba lalle bane jam'iyyar da ke kan mulki ta ci gaba da zama a kan karaga bayan an yi zabe". in ji masanin.

Ya ƙara da cewa ba ya tsammanin jam'iyya ko ma wani shugaba sai ya yi shekara da shekaru a kan karagar mulki ne kawai zai iya aiwatar da manufofinsa da kuma cimma bukatun al'umma da kuma na jam'iyya.