Hotunan Afurka na mako 19-25 Maris 2021: Masoya balan-balan, wasa a cikin ƙanƙara

Wasu daga cikjin ƙayatattun hotunan sassa daban-daban na Afirka:

Wani mutum rike da tarin balan-balan da ake bai wa 'yan uwa da abokan arziki a kofar ofoshin magajin garin Bangui , a jamhuriar tsakiyar Afurka a ranar Lahadi 20 Maris 2021.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana miƙa wa masu halartar wani biki balan-balan a birnin Bangui na Jamhuriyar Tsakiyar Afirka a ranar Lahadi.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wata yarinya da ta yi matukar kyau sanye da takunkumi ruwan hoda, lokacin da suka koma makaranta a birnin Maputo na kasar Mozambique, ranar Litinin.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Afirka Ta Kudu maƙwabciyar Zimbabwe ma dalibai ne suka koma makaranta a dai ranar Litinin bayan kullen annobar cutar korona.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yara na wasan kwallon teburi a ranar Juma'a a garin Mopti na kasar Mali, mai iyaka da Jamhuriyar Nijar da kogin Bani.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Yara na jin dadin wasan zamiyar ƙanƙara ranar Litinin a tsaunin Chrea na Algeria.....

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wurin da ake ajiye abin hawa zamiyar kankara, mai nisan kilomita kusan 60 daga kudancin babban birnin kasar, Algiers.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mai son kwallon kafa sanye da jesi dauke da lambar dan wasan Barcelona Lionel Messi, zaune a kwale-kwalen kamun kifi a gabar teku a kasar Liberiya ranar Lahadi...

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mutane a cikin kwale-kwalen kamun kifin da aka yi wa kwalliya da tambarin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona....

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Duk wani gini ko allo da ke gabar ruwan Lako Piso an yi masa ado da tambarin kungiyar kwallon kafa ta FCB, cikin launuka daban-daban.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ranar Laraba, yar wasar gaba ta kungiyar Barcelona kuma 'yar Najeriya Asisat Oshoala, na taimaka wa kungiyarta zura kwallo a ragar Manchester City, a wasan gab da na kusa da na karshen gasar Champions League a kasar Italiya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gabannin wannan rana, dan wasan tseren keke dan Eritrea, Merhawi Kudus Ghebremedhin ya shiga tseren Volta a Catalunya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wata mace tana wuce wani gini da aka kawata da garin Figuig da ke bakin ruwa a kasar Moroko a ranar Juma'a.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An gina garin ne a kusa da gabar ruwa, kewaye da bishiyoyin dabino a kusa da iyakar Moroko da Algeria…

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A kwanakin baya an yi zanga-zanga a garin, kan matakin gwamnatin Algeria na korar masu shuka dabino daga yankin da suka dade suna amfani da shi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Litinin mai kula da horas da dawakan yankin Larabawa ne yake bai wa daya daga cikin dawakansa magani a birnin Bengazi na kasar Libya.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A dai wannan ranar a yammacin kasar Libya, an harba bindigar tankar yaki lokacin bikin yaye wadanda alhakin gadin gabar teku da tsare yanki mai arzikin mai a kasar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yara cikin annashuwa a cikin a kori-kura sun wuce rakuman da ke tsere a kusa da birnin Omdurman na Sudan a ranar Juma'a...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Iyalai masu kiwon rakuma ne suka shirya tseren rakuman a kauyen al-Ikhlas.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A dai ranar Juma'ar, wasu maza na jira don cika tukwanen gas da za su kai asibiti don taimaka wa 'yan uwansu masu fama da cutar korona, a wani yanki na birnin Addis Ababa a kasar Habasha.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Omar Sayed Shaaban kenan dan kasar Masar mai wasan ninkaya, sanye da hular roba ya na atisaye cikin wani kwamin wanka a birnin Alkhahira ranar Lahadi. A farkon wannan watan ya kafa tarihi a duniya na wanda ya fi kowa yin tsalle mai nisa tare da fadawa cikin ruwa.

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka.