Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama fasto biyu da zargin kisan jami'anta a kudancin ƙasar

Mohammed Adamu

Asalin hoton, NG Police

Bayanan hoto,

Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu ya ce 'babu mai laifin da zai tsere wa hukuma'

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum 16 da take zargi da kashe jami'anta a yankin kudu maso gabashin ƙasar.

Wata sanarwa da Frank Mba mai magana da yawun rundunar ya fitar ranar Lahadi, ta ce wasu daga cikin waɗanda aka kama sun amsa laifin kasancewarsu mambobin ƙungiyar IPOB da kuma ESN, waɗanda ke fafutikar kafa ƙasar Biafra.

Frank Mba ya ce an kama wani fasto mai suna Cletus Nwachukwu Egole na Cocin Holy Blessed Trinity Sabbath da wani faston mai suna Michael Uba na ƙungiyar Association of Jewish Faith a Jihar Imo da zargin taimaka wa waɗanda ake zargin.

"Cletus Nwachukwu, wanda aka fi sani da Alewa, da Michael Uba, su ne ke tsara hare-hare kan jami'an tsaro da kuma bai wa gungun mutanen mafaka," a cewar sanarwar.

Ta ƙara da cewa: "Ana amfani da gidan Cletus Nwachukwu a matsayin wurin tsara hare-hare sannan ya sadaukar da gonar ɗan uwansa domin amfani da ita wajen bayar da horo da mafaka ga miyagu."

An kashe 'yan sandan Najeriya fiye da 10 a watan Maris sakamakon hare-haren 'yan bindiga a yankin na kudu maso gabas.

Haka nan, an ƙona caji ofis da yawa a hare-haren. 'Yan sanda sun ce an kama mutanen ne a yankuna daban-daban bisa laifuka a wurare daban-daban.

Rundunar ta gano tare da ƙwace bindiga ƙirar AK-47 guda tara da wasu guda biyar da ababen fashewa guda 10 da wayoyin oba-oba daga hannun mutanen.

Laifukan da ake zargin mutanen da aikatawa

Asalin hoton, NG Police

Bayanan hoto,

Makaman da aka ƙwace daga hannun waɗanda ake zargin

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

'Yan sanda sun bayyana mutum huɗu a matsayin jagororin waɗanda ake zargi da kisan, waɗanda suka fito daga jihohin Abia da Cross River da Imo.

Mutanen su ne: Ugochukwu Samuel (Biggy) mai shekara 28; Raphael Idang mai 31; Cletus Nwachukwu Egole (Alewa) mai 60; Michael Uba mai shekara 33.

Sai kuma sauran mutum 12, waɗanda ta ce ana zargi da kashe jami'anta a jihohin kudu maso gabas.

"Bincike ya nuna cewa Ugochukwu Samuel da Raphael Idang na cikin miyagun da suka kai wa 'yan sanda hari ranar 24 ga Disamban 2020 a kan Titin Orlu-Ihiala na Imo, inda suka kashe 'yan sanda biyu kuma aka ƙona motarsu ƙirar Hilux," in ji rundunar.

"Dukkansu biyun na cikin waɗanda suka kai wa 'yan sandan sintiri hari ranar 13 ga Janairun 2021 tare da kashe mutum ɗaya."

An kama Ugochukwu Samuel ne yayin da ya je wani asibiti neman magani sakamakon raunin da ya ji a wani hari da tawagarsa ta kai kan sojoji, inda suka kashe wasu kuma suka ɗebe makamansu, a cewar 'yan sandan.

Rundunar ta ƙara da cewa mutum biyun sun amsa laifin kasancewarsu mambobin ƙungiyoyin Indigenous People of Biafra (IPOB) da Estern Security Network (ESN).

A watan Satumban 2017 ne wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta haramta ayyukan ƙungiyar IPOB kuma ta bayyana ta a matsayin ta "yan ta'adda".