Muhammadu Buhari: Shugaban Najeriya zai tafi London domin a duba lafiyarsa

P

Asalin hoton, Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu zai tafi birnin Londan da ke kasar Birtaniya domin a duba lafiyarsa.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ranar Litinin da maraice, ta ce shugaban na Najeriya zai tafi birnin London ranar Talata domin ya ga likita.

Mai magana da yawun shugaban Najeriyar Mallam Garba Shehu ya shaidawa BBC cewa dama shugaba Buhari ya sha yin irin wannan tafiya don haka ba wani sabon abu bane.

Ya kuma kara da cewa babu wata matsala da ta taso ta rashin lafiya a yanzu da za a ce ita ce ta janyo yin wannan tafiya.

Fadar shugaban Najeriyar ta ce shugaban zai ci gaba da kasancewa a matsayinsa ba tare da ya miƙawa mataimakinsa mulki ba.

Shugaba Buhari zai yi tafiyar ne a yayin da kungiyar likitoci ta sha alwashin soma yajin aiki ranar 1 ga watan Afrilu saboda rashin kayan aiki da isasshen albashi.

Shugaban Najeriyan ya sha tafiya Landan domin duba lafiyarsa tun lokacin da ya fara jagorantar kasar.

A 2017, Shugaban ya kwashe kwanaki 150 a Burtaniya a wata tafiyar duba lafiyar da ba a bayyana abin da ke damun shi ba.

Buhari ya kara komawa Burtaniya a watan Mayun 2018 domin ganin liktansa, inda ya yi kwana hudu kacal a kasar.

A watan Nuwambar 2020 ne, mai dakin shugaban kasar Aisha Buhari, ta ce akwai bukatar inganta bangaren lafiya a Najeriya domin a rage tafiye-tafiyen neman magani kasashen waje.