An ji ƙarar harbe harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa a Nijar

Sojojin Nijar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kwashe kusan minti 15 ana harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Ƙasar Nijar

Sojan da ake zargi da jagorantar juyin mulki a Jamhuriyar Nijar a daren Laraba ya tsere, a cewar kafofin yaɗa labaran Faransa.

"A cewar bayanan farko-farko, wani sojan sama mai suna Kaftin Gourouza, shi ne shugaban maharan waɗanda suka isa a motoci guda huɗu," a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP yana mai ambato gidan rediyon RFI.

"Shugaban nasu wanda yanzu haka ake nemansa ruwa a jallo, ya tsere, a cewar majiyoyin tsaro."

Wata majiyar tsaro ta shaida wa AFP cewa an kama wasu sojoji biyo bayan yunƙurin juyin mulkin.

Gwamnatin kasar ta tabbatar da yunƙurin juyin mulkin yayin da aka sanya birnin Yamai a cikin shirin ko-ta-kwana.

Tun misalin ƙarfe 3:00 na tsadar dare aka fara jin harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Ƙasa kuma an ɗauki kusan minti 15 ana yi.

Jami'an tsaron fadar ne suka daƙile yunƙurin, wanda ya faru ƙasa da kwana biyu kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Mohamed Bazoum.

Wasu ofisoshin jakadancin ƙasashen waje da ke birnin na Yamai sun yi kira ga ma'aikatansu da su zauna a gida.

Gidan rediyon ƙasar mallakar gwamnati da ke birnin na Yamai na ci gaba da watsa shirye-shiryensa ba tare da wata tangarda ba.

Tarihin Nijar wadda ke ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya talauci a duniya, cike yake da juyin mulki na soja da kuma hare-haren 'yan bindiga masu iƙirarin jihadi da ke sanadiyyar rasa rayuka.

Martanin gwamnatin Nijar

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce tuni ta soma gudanar da bincike kan yunkurin juyin mulkin wanda bai yi nasara ba.

A wani taron manema labarai da ya gudanar, ministan watsa labaran kasar Abdurrahman Zakriyya ya ce "cikin daren 30 wayewar garin 31 ga watan Maris ne aka yi nasarar barar da yunkurin juyin mulki da aka shirya. Tuni aka fara bincike domin gano masu hannu cikin aikata wannan lamari don mika su ga shari'a."

Ya kara da cewa an kama da dama daga cikin mutanen da suka kitsa juyin mulkin yana mai cewa an shirya shi ne daga ciki da ma wajen kasar.

Minista Abdurrahman Zakriyya ya ce gwamnati ta jinjina wa dakarun tsaron da ke fadar shugaban kasar da wadanda suka dafa musu wajen murkushe yunkurin juyin mulkin.

Me masu sharhi ke cewa?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

BBC ta tuntubi Dakta Gambo Alhaji Sani, wani masanin siyasa a Zinder don jin yadda yake kallon wannan harbe-harben da aka yi da wasu ke zargin ko yunkurin juyin-mulki ne a kasar.

Ya ce "kawo yanzu hukumomi ba su yi bayani a hukance kana bin da ya faru ba, amma wasu na ganin wata makarkashiya ce ta hana zanga-zangar da aka shirya yi a ranar Laraba.

''Amma idan ya kasance cewa da gaske yunkurin juyin mulki ne, to tabbas dimokradiyyarmu gurguwa ce.

"Ya nuna ba a mutunta doka, da ta ce a bai wa al'umma abin da suka zaba na shugaban kasa, sannan mafarkin da ake yi na cewa juyin-mulki ya zama tarihi a jamhuriyar Nijar ya kau ba.''

Ya kara da cewa ba a san al'ummar Nijar ko 'yan siyasa da tashin hankalin bayan zabe ba, yawanci da zarar an sanar da sakamakon zaben wanda ya sha kaye na kiran dan uwansa ya masa murna da fatan alkhairi.

Sai dai a wannan karon hakan bai samu ba, duba da yadda aka shirya zaben.

''Tun da aka kada gangar siyasa shekara biyu da suka wuce ake zaman doya da manja tsakanin 'yan hamayya da 'yan mulki, kan tababa akan takarar madugun adawa Hama Amadu da Bazoum Muhammad da kotu ta sanar ya yi nasara.

''Aka zo aka dora hukumar zaben da dukkan bangarorin ba su aminta da ita ba, Kotun Ƙoli ma wani bangare bai amince da shi ba. Wannan na daga cikin abin da ya kara rura rikici tsakanin bangarorin biyu.''

Ya ce mafita a nan ita ce a mutunta doka, muddin masu mulki da 'yan adawa ba za su mutunta dokokin dimokradiyya ba tabbas za a ci gaba da ganin irin wannan matsala.