Mathew Kukah ya sake caccakar gwamnatin Buhari

Bishop Kukah
Bayanan hoto,

Bishop Kukah

Bishop din darikar katolika na Sakkwato, Mathew Kukah, ya sake caccakar gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Muhammadu Buhari kan tababbarewar tsaro a kasar.

Mista Kuka ya soki gwamnatin Najeriyar a sakonsa na Easter.

A sakon mai taken "Najeriya: kafin daukakarmu ta tafi", Bishop Kukah ya yi waiwaye ne kan halin da Najeriya da 'yan kasar ke ciki a yanzu.

Mista Kukah ya ce Najeriya ta zama "filin da ake kashe dimbin mutane saboda gwamnati da wadanda suke karkashin gwamnati sun zuba ido suna kallo ba tare da yin komai ba".

"Wani gajimeren girgije mai dimautarwa na yanke kauna tare da janyo damuwa da bakin ciki da wahala. Ba mu da wani sako kuma ba mu da masaniya game da tsawon lokacin da wannan zai ci gaba. Mutanenmu suna neman kwanciyar hankali da kariya amma takaici da duhu na barazanar nutsar da su." In ji sa.

Wani bangare na sakon ya kuma cen: makomar kasar tana cikin hadari, kasar ta soma wargajewa. Rashin tsaro da ake ci gaba da fuskanta wanda ba a magance ba ya bar bakin ciki da ra'ayoyi masu hadari a kan cewa wadanda suke da ikon tabbatar da tsaron kasar ko dai ba za su iya ba ko ba sa son su sauke nauyin da ya rataya a kansu".

Limamin ya karkare da cewa yayin da matsalolin Najeriya ke karuwa a ko yaushe, ya kamata 'yan kasar su dage da addu'a.