IPOB: Rundunar 'yan sandan Najeriya ta zargi 'yan ƙungiyar da kai hari kan jami'anta a Jihar Imo

Owerri prison

Hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya ta ce 'yan bindiga sun kubutar da fursunoni 1,844 daga gidan yarin birnin Owerri na jihar Imo.

Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta Francis Enobore ya fitar ranar Litinin.

Hukumar ta fitar da sanarwar ce a yayin da rundunar 'yan sandan kasar ta dora alhakin kai hari kan hedikwatarta da kuma gidan yarin birnin Owerri kan 'yan kungiyar IPOB ranar ta Litinin da asubahi.

'Yan bindigar sun yi amfani da manyan bindigogi masu sarrafa kansu da nakiyoyi wajen fasa gidan yarin, a cewar hukumar.

"A kididdiga ta karshe, fursunoni 6 sun dawo don radin kansu cikin gidan yarin yayin da fur 35 suka ki amincewa su tsere a yayin harin", in ji sanarwar.

'Yan IPOB ne suka kai harin Jihar Imo - 'Yan sanda

Asalin hoton, Getty Images

Sufeto Janar na 'yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu ya ba da umarnin aikewa da wasu karin 'yan sandan kwantar da tarzoma zuwa Jihar Imo, inda aka ƙona ofishin 'yan sandan a safiyar Litinin 5 ga watan Afrilun 2021.

Kazalika, rundunar ta ce binciken farko-farko da ta gudanar ya nuna cewa 'yan bindigar da suka kai harin mambobin ƙungiyar IPOB ne masu fafutikar ɓallewa daga Najeriya tare da kafa ƙasar Biafra.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Frank Mba ya fitar, Mohammed Adamu ya ce an aike da karin 'yan sandan ne domin kara karfafa tsaro a jihar da kuma kauce wa sake faruwar wani harin kan jami'an tsaro da kadarorin gwamnati.

Sanarwar ta ce: "Binciken da aka fara gudanarwa ya gano cewa maharan da suka kai harin suna da yawa kuma dauke da muggan makamai irin su AK-47 sannan kuma mambobi ne na kungiyar IPOB".

Ta kara da cewa, kokarin maharan na kutsawa wurin ajiyar makaman hedikwatar ya ci tura biyo bayan dagewar da jami'an da suke aiki suka yi na hana su shiga cikin wurin tare da sace makaman da ake ajiye da su.

Ba a samu nasarar shiga wurin ba kuma kwansitabil daya ne ya ji rauni a kafadarsa, a cewar sanarwar.

Haka nan, 'yan sanda sun samu nasarar kwace wata mota da maharan suka kai harin da ita, kuma za a gudanar da bincike mai tsauri a kanta.

Sufeto janar din wanda ya yi Allah-wadai da harin, ya kuma umarci kwamishinan 'yan sandan Jihar Imo da tawagar da aka aike jihar su gudanar da bincike domin gano maharan tare da tabbatar da cewa sun girbi abin da suka shuka.

Rundunar 'yan sandan ta ce shugaban ya yi kira ga 'yan kasar su rika taimaka wa 'yan sanda da jami'an tsaro da bayanan da suka kamata domin ganowa da kuma kama masu laifi.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tunda farko rahotanni daga Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a hedikwatar rundunar 'yan sanda da wani gidan yari da ke Owerri babban birnin jihar.

Ganau sun shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne daga tsakar daren jiya Lahadi zuwa Litinin da safe.

Rahotannin sun kara da cewa 'yan bindigar, wadanda ake zargi 'yan kungiyar IPOB ce da ke fafutukar ballewa daga Najeriya, sun kubutar da fursunoni da dama daga gidan yarin.

Ba a san adadin fursunonin da ke gidan yarin a lokacin da aka kai harin ba.

Sai dai a bara kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce ana tsare da mutum 2156 a gidan yarin da aka gina domin daure mutum 548.

Wani mazaunin birnin mai suna Paul ya shaida wa BBC cewa karar harbe-harben bindiga ta hana su bacci a daukacin daren Lahadi.

Wakilin BBC a birnin ya ruwaito cewa an kashe mutum daya yayin da aka kona motoci fiye da 30 sakamakon yamutsin.

Sai dai mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Orlando Ikeokwu bai amsa kiran wayar da muka yi masa ba domin karin bayani kan lamarin.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun yi amfani da nakiya da bindigogi masu sarrafa kansu wajen kai harin.

"Sai dai wasu daga cikin fursunonn sun ki yarda a kubutar da su yayin da wasu da aka kubutar suka dawo da kansu," a cewa majyar PRNigeria.

A baya bayan nan dai masu fafutukar ballewa daga Najeriya sun matsa kaimi wajen kai hare-hare a kudu maso gabas da kudu maso kudancin kasar.

A makon jiya an kama mutane da dama da ake zargi da kai hari kan 'yan sanda da ma ofisoshinsu lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaro da dama.

Hotunan harin da aka kai kan gidan yari da hedikwatar