Amnesty ta ce korona ta fito da bambancin da ake nunawa a duniya

Kasashe masu arziki sun saye mafi yawan allurar riga kafi sun kyale matalauta

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto,

Kasashe masu arziki sun saye mafi yawan allurar riga kafi sun kyale matalauta

Kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya, ta Amnesty International, ta ce annobar korona ta fito da bambancin da ake da shi a duniya fili karara.

Rahoton kungiyar na shekara ta 2020 da aka wallafa, ya ce annobar ta yi tasiri mafi muni a kan mutanen da suka fi rauni.

Sannan kuma kungiyar ta soki Birtaniya, wadda ta ce ta kama hanyar da ba ta dace ba a kan batun mutunta hakkin dan adam.

Rahoton ya nuna cewa annobar ta duniya a iya cewa ta shafi kusan kowa da kowa, to amma tasirinta ko alama bai kasance raba daidai ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutane mafiya rauni illar annobar ta fi shafa

Kungiyar ta Amnesty ta ce, rukunin mutanen da aka fi nuna wa wariya wadanda suka hada da mata da 'yan gudun hijira, su ne suka fi dandana kudarsu kan annobar.

Suma, ma'aikatan lafiya da ma'aikata 'yan ci-rani ba a tallafa musu- ba su tsira ba daga wannan bambanci na samun kulawa daga illar annobar ta korona in ji kungiyar.

Babbar Sakataiyar kungiyar ta Amnesty, Agnès Callamard, ta yi kakkausar suka ga kasashe masu arziki a kan rashin yin abin da ya dace na taimaka wa kasashe marassa arziki wajen yi wa al'ummarsu allurar riga kafin koronar:

Ta ce: " Kasashe da suka fi arziki sun sayi mafi yawan allurar riga kafin. Sun yi wa al'ummarsu riga kafin. Hakan ya yi daidai. To amma. Abin kaico da takaici ta fanni da dama, da kamata ya yi a ce sun yi tunanin duniya baki daya, amma ba su yi hakan ba''.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ma'aikata 'yan ci-rani na daga wadanda aka fi rashin ba wa kulawa ta kariya daga annobar

Haka kuma rahoton na Amnesty ya nuna karuwar cin zarafin mata a gida a Birtaniya, kamar yadda yake a bayanan da aka tattara na sauran kasashen duniya. Cin zarafin mata ya karu, wanda karuwar kadaicewa ko zaman tare da aka samu tsakanin matan da masu gallaza musu a lokacin annobar ne ya kara yawan ta'adar.

Rahoton ya kuma fito fili da abin da ya kira kokarin amfani ko fakewa da halin da ake ciki na annobar wajen take hakkin dan adam.

Inda ya nuna cewa shugabanni a kasar Hungary da yankin tekun Persia, sun bullo da sabbin dokoki na yaki da yada labaran karya, sannan kuma gallazawar da China ke yi wa Musulmi 'yan kabilar Uighur ta karu.

Asalin hoton, WIKIPIDIA

Bayanan hoto,

Kungiyar Amnesty International ta ce annobar korona ta fito fili da bambancin da ake nuna wa matalautan kasashe

Rahoton ya nuna cewa a Birtaniya sabon kudurin dokar da gwamnati ta bullo da shi kan 'yan sanda da aikata miyagun laifuka, da dauri da kotuna na barazanar takaita damar da jama'a ke da ita ta yin zanga-zangar lumana.

Darektar kungiyar ta Amnestry a Birtaniya Kate Allen, ta ce bayan miyagun kurakuran da gwamnatin Birtaniya ta rika yi daya bayan daya a lokacin annobar, a yanzu kuma gwamnatin na kokarin raba jama'a da 'yancin da suke da shi na kalubalantar duk wani hukunci ko mataki da ta dauka.