Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Dembele, Aguero, Konate, Lingard, Lacazette, Sabitzer, Walcott

Sergio Aguero ne ya fi ci wa Manchester City kwallo a tarihi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sergio Aguero ne ya fi ci wa Manchester City kwallo a tarihi

Dan wasan gaba na Manchester City Sergio Aguero, mai shekara 32, na son kara matsayinsa a jerin wadanda suka fi yawan cin kwallo a Premier, wanda hakan zai iya taimaka wa Chelsea a kokarin da take na sayen dan wasan na Argentina, idan lokacin zamansa a City ya kare a bazaran nan kamar yadda jaridar Evening Standard ta ruwaito.

Aguero na son kauce wa shiga wasannin gasar cin kofin Zakarun Turai a kaka ta gaba domin ya ci gaba da zama a gasar Premier inda Chelsea da Tottenham ke daga cikin kungiyoyin da zai duba yuwuwar tafiya.Telegraph ce ta ruwaito labarin

Watakila Manchester United ta bi layin Liverpool a fafutukar neman sayen dan bayan RB Leipzig, dan Faransa Ibrahima Konate. Ana sa ran dan wasan mai shekara 21 ya kai farashin kusan fam miliyan 34. In ji Eurosport.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Maiyuwuwa Man Utd ta bi sahun Liverpool na son sayen Ibrahima Konate, dan Faransa

West Ham za ta yi yunkurin tabbatar da zaman dan wasan tsakiya na ingila Jesse Lingard, zaman dindindin a kungiyar, amma kuma tana fargabar cewa Manchester United da ta ba ta aronsa za ta nemi ta biya makudan kudade a kan dan wasan mai shekara 28, kamar yadda jaridar Mail ta labarto.

Arsenal za ta duba yuwuwar sayar da dan wasan gabanta na Faransa Alexandre Lacazette a lokacin kasuwar sayar da 'yan kwallo ta bazara. Tuni kungiyoyi da dama suka nuna sha'awarsu ta sayen dan wasan mai shekara 29, wadanda suka hada da Inter Milan da Roma da Sevilla da kuma Atletico Madrid, kamar yadda labarin ya fito daga 90min.

Tottenham na shirin sayen dan wasan tsakiya na RB Leipzig Marcel Sabitzer, dan Austria mai shekara 27. A ruwayar jaridar Football Insider

Juventus da Arsenal da kuma Chelsea na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na AC Milan Hakan Calhanoglu, dan Turkiyya mai sheakara 27, wanda kila ya kasance bas hi da wata kungiya a karshen kakar da ake ciki, kamar yadda Sky Sports ta bayar da labarin.

Dan wasan gaba na Ingila Theo Walcott, mai shekara 32, zai yi zaman dindindin a Southampton daga lokacin bazara lokacin da wa'adinsa na aro a kungiyar da Everton bayar da shi zai kare. In ji Talksport

Mai horad da Barcelona Ronald Koeman ya bukaci dan wasan gaba na Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23, da ya zauna a kungiyar duk da sha'awar da Manchester United ke nuna a kansa. In ji jaridar .Metro.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ronald Koeman ba ya son Dembele tafi

Manchester City na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Sheffield United Sander Berge, dan Norway mai shekara 23, a kokarin da kungiyar take yin a maye gurbin dan Brazil Fernandinho, mai shekara 35. Kamar yadda jaridar Voetbal24 ta harshen kasar Holland ta ruwaito.

Mahaifin dan wasan tsakiya Lucas Torreira ya nemi Arsenal da ta bar dan wasan na Uruguay mai shekara 25, wanda ke zaman aro a Atletico Madrid, ya bar kungiyar a bazaran nan mai zuwa. Gidan Radio Continental ne ya ruwaito labarin ta jaridar Mirror.

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Arsenal ta bayar da aron Lucas Torreira ne ga Atletico Madrid

Dan wasan Villarreal na gaba Gerard Moreno na daga cikin fitattun 'yan wasan da Atletico Madrid ke harin saye a bazara, sai dai kuma yarjejeniyar dan wasan na Sifaniya mai shekara 28 ta tanadi biyan fam miliyan 85.6 ga duka mai son daukarsa.In ji jaridar Marca