Akwai muggan makamai miliyan shida a Najeriya - Abdussalam Abubakar

Asalin hoton, Rauf Aregbesola Twitter
Tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar ya alakanta karuwar tashe-tashen hankula a kasar da yawaitar yawaitar makamai da aka samu a hannun ɗai-ɗaikun mutane, inda ya ce akwai a ƙalla makamai miliyan shida da ke yawo a hannun mutane ba bisa ƙa'ida ba.
Abdulsalami wanda kuma shi ne shugaban kwamitin zaman lafiya na ƙasar ya bayyana hakan ne yayain wani taron tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki da ya gudana a ranar Laraba a Abuja.
A cewarsa, shigowar bazuwar makaman wanda ya haifar da matsalar tsaro a Najeriya ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 80,000.
Manyan mutane da dama sun halarci taron wadanda suka hada da shugaban cocin katolika na Sokoto, Matthew Kukah da Sarkin Musulmai Sultan Sa'ad Abubakar III; da shugaban kungiyar gwamnonin arewa Simon Lalong da Aliko Dangote da sauran mambobin kwamitin.
Ya ce, "Bazuwar muggan makamai a baki ɗayan Najeriya abin damuwa ne. An yi ƙiyasin cewa akwai fiye da makamai miliyan shida da suka yaɗu a ƙasar nan.
"Wannan rikici na matsalar tsaro ya hallaka mutum 80,000 sannan ta raba kusan wasu miliyan uku da muhallansu," in ji Abdulsalami.
Shi ma tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon ya shawarci 'yan Najeriya cewa a ajiye maganar addini da kabilanci a san cewa matsalar Najeriya ta duka 'yan kasar ce.
Wasu manyan matsalolin Najeriya da Abdussalami ya zayyana
- Rikicin Boko Haram
- Fashi da makami
- Ƙaruwar talauci
- Yunwa saboda barazanar da manoma ke fuskanta
- Rashin zuba isassun kuɗaɗe a fannin tsaro, inda Janar Abdussalami ya ce jami'an tsaro za su iya abin a zo a gani idan aka saya musu manyan makamai.
Abin da wasu masu ruwa da tsakin suka ce
Shi ma tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon kira ya yi ga yan ƙasar da su ajiye bambance-bambancen addinai da na siyasa su mayar da hankali kan matsalolin da ƙasar ke fama da su su kuma magance su tare.
Mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka Aliko Ɗangote cewa ya yi ya kamata kafofin yada labarai su dinga taka tsan-tsan da irin labaran da suke yaɗawa saboda gudun tsoratar da kuma korar masu zuba jari da ke son yin kasuwanci a kasar.
Ya ƙara da cewa babu wanda zai iya samun sukunin aiwatar da hidimomin gabansa da suka haɗa da kasuwanci idan har babu cikakken tsaro.






