Rawar ballet da tattaki a gaɓar teku cikin hotunan Afirka na mako: 2 zuwa 8 fa Afrilu 2021

Kyawawan hotuna daga sassa daban-daban na Afurka a mako:

Mata da miji, da tgwayen 'ya'yansu, sanye da kayan ninkaya su na tattaki a gabar teku. m

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wasu ma'aurata na tattaki a gabar tekun Saly, da ke Senegal, ranar Lahadi.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A ranar Alhamis, masu rawar ballet suka yi atisaye na karshe a dandamalin Joburg gabannin fara gasar rawar a Afirka Ta Kudu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Haka ma Afirka Ta Kudun, an kunna kyandira ranar Juma'a mai tsarki da mabiya addinin kirista suka yi addu'o'i a yankin Soweto.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Kwana biyu bayan nan, an gudanar da bikin Easter, a ranar Lahadi an gudanar da addu'o'i a Majami'ar La Paroisse Saint Aloys d'Ijenda a Burundi.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A wannan ranar amma a birnin Lagos din Najeriya, mata na gudanar da addu'o'i a Majami'ar Celestial Church of Christ.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Can a Senegal kuwa, mabiya darikar Katolika sun wuce wani doki da ke kallonsu.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mabiya addinin Kirista sun yi layi a gaban malamin coci a Majami'ar Saint-Augustin a La Goulette da ke Tunis, a Tunisia

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mabiya addinin kirista sun gudanar da shagulgula a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a Majami'ar International Kimbanguist, wadda aka samar da ita sama da shekaru 100 da suka wuce, lokacin bikin tuna wa da lokacin Shugaba Félix Tshisekedi ya halarta.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wani mutum ya wuce zanen wata mace a birnin Johannesburg, na Afurka Ta Kudu, ranar Laraba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Laraba, wata manomiya na kallon tarin ganyen taba, a daidai lokacin da aka fara kakar saida mahadin taba sigari a Zimbabwe.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Lahadi dan rawa sanye da tufafin gargajiya na Misrawa, yana daukar hoton dauki da kanka, lokacin da aka kwashe gawawwakin sarakuna 22 daga tsohon gidan adana kayan tarihi zuwa sanon da aka gina.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A ranar Talata, wani malamin makaranta da ake tsare da shi ya yi wa mai daukar hoto alamar nasara da hannunsa, a lokacin zanga-zanga da ma'aikata suka yi kan karin albashi a birnin Rabat na Moroko

Dukkan hotunan su na da hakkin mallaka.