PDP: Rabiu Musa Kwankwaso da Aminu Waziri Tambuwal na musayar kalamai

Kano

Asalin hoton, Facebook/Kwankwaso

Da alama wata baraka ta kunno kai a reshen jamiyyar PDP na arewa maso yammacin Najeriya, inda daya daga cikin iyayen jam'iyyar a yankin Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnan jihar Sokoto Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da yin katsalandan cikin al'amuran jam'iyyar a jihar Kano.

A cewar Kwankwaso wanda yake jagorantar bangaren Kwankwasiyya ya zargi Tambuwal da hada kai da wasu ƴaƴan jam'iyyar na Kano da ke hamayya da shi da mutanensa don taimaka musu su samu shugabancin jam'iyyar na yankin Arewa maso Yamma.

"Abin takaici shi ne akwai shi gwamna na Sokoto, wanda a ra'ayinsa bai kamata mu musamman yan Kwankwasiyya a ba mu wadannan mukamai ba,"in ji Kwankwaso.

To sai dai a nasa bangaren, gwamna Aminu Tambuwal ya musanta wannan zargin inda ya ce "duk wanda yake da sha'awa ya fito ya yi takara."

Ya kuma nisanta kansa da zargin da Kwankwaso ya yi masa cewa yana da hannu a saya wa Sanata Bello Hayatu Gwarzo fom.

Ga karin bayani cikin rahoton Yusuf Ibrahim Yakasai:

Bayanan sauti

Rahoton Yusuf Ibrahim Yakasai