Musulmin Afirka za su yi azumin Ramadana na biyu cikin annoba

Azumin watan Ramadan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Azumin watan Ramadan

Musulmi a duk fadin Afirka za su fara azumin watan Ramadan mai alfarma wanda zai fara daga ranar Talata.

A shekara ta biyu, dokokin takaita taruwar jama'a na ci gaba da aiki cikin wasu ƙasashe a cikin watan azumin Ramadana.

Kasar Masar ta hana yin sallar jam'i a masallatai.

Firaministan Tunisia Hichem Mechichi ya goyi bayan shawarar tsawaita awanni na dokar hana fitar dare a ranar Lahadi, bayan damuwar da aka nuna ga rayuwar mutane.

Mista Mechichi, wanda ya dade yana rashin jituwa da Shugaba Kaïs Saïed, a ranar 7 ga Afrilu ya ba da sanarwar cewa dokar hana fita da aka sanya domin dakile yaduwar annobar korona za ta fara ne daga karfe 7 na yamma agogon kasar (18:00 GMT), maimakon 10 na dare gabanin Ramadan.

Bayan kwana biyu, Mista Saïed ya yi kira ga Firai Minista da ya sake nazarin shawarar, don kauce wa asarar dubban ayyuka a cikin watan mai alfarma wanda Musulmi ke azumi a ciki har faduwar rana.

A bara, shugabannin Afirka sun aike da sakonnin Ramadan na musamman na fatan alheri ga Musulmin da ke nahiyar yayin da aka zartar da dokokin dakile bazuwar cutar korona masu tsauri.