Buhari ya dawo daga London bayan mako biyu

Buhari

Asalin hoton, Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Najeriya daga London a ranar Alhamis da yamma.

Mai taimaka wa shugaban kan yada labarai Malam Garba Shehu ne ya tabbatar wa da BBC labarin.

Shugaba Buhari ya tafi birnin Londan da ke kasar Birtaniya ne ranar 30 ga watan Maris domin a duba lafiyarsa.

Manyan jami'an gwamnatin ƙasar da shugabannin rundunonin tsaro da wasu ministoci na daga cikin waɗanda suka tarbi shugaban a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Shugaba Buhari ya sha yin irin wannan tafiya don jinya ko duba lafiyarsa, "don haka ba sabon abu ba ne," kamar yadda Garba Shehu ya fada gabanin tafiyar shugaban.

Ko a jiya Laraba Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ministan yaɗa labarai da al'adu Lai Mohammed, ya yi tsokaci kan ranar dawowar shugaban a taron majalisar zartwarwa da aka gudanar a Abuja.

Sai dai kuma a makon da ya gabata kakakin shugaban Malam Garba Shehu ya fitar da wata wasika zuwa ga sarkin Jordan, yana mai cewa Buhari ya je London ne domin gajeren hutu.

Tafiyar Shugaban ta janyo ce ce-ku ce da zanga-zanga tsakanin masu adawa da magoya bayansa a Landan.

Shugaba Buhari ya yi tafiyar ne a yayin da kungiyar likitoci ta sha alwashin soma yajin aiki ranar 1 ga watan Afrilu saboda rashin kayan aiki da isasshen albashi, sai dai daga bisani ta janye.

buhari

Asalin hoton, Presidncy

Buhari

Asalin hoton, Presidency

Shugaban Najeriyan ya sha tafiya Landan domin duba lafiyarsa tun lokacin da ya fara jagorantar kasar.

A 2017, Shugaban ya kwashe kwanaki 150 a Burtaniya a wata tafiyar duba lafiyar da ba a bayyana abin da ke damunsa ba.

Buhari ya kara komawa Burtaniya a watan Mayun 2018 domin ganin likitansa, inda ya yi kwana hudu kacal a kasar.

A watan Nuwambar 2020 mai dakin shugaban kasar Aisha Buhari, ta ce akwai bukatar inganta bangaren lafiya a Najeriya domin a rage tafiye-tafiyen neman magani kasashen waje.