Yadda za a gwangwanje makafi da sandunan zamani a Najeriya

Wata ƙungiya da ke taimaka wa masu larurar nakasa a Najeriya ta ce za ta raba sandunan jagora ga masu fama da larurar gani 10,000 a wasu sassan ƙasar.
Ƙungiyar mai suna 'Disability Resource Foundation of Nigeria' ta ce za ta raba sandunan jagora ne ga masu gani garara-garara da kuma marasa gani.
A cewarta ta bijiro da wannan tsarin ne da nufin rage musu haɗuran da sukan fuskanta a yayin zirga-zirga da kuma sanya su zama masu dogaro da kansu.
Shugaban ƙungiyar Salisu Ibrahim ya shaida wa BBC cewa ɗaya daga cikin abubuwan da suka ja hankalinsu wajen ƙaddamar da wannan shiri shi ne burinsu na tabbatar da cewa kowanne mai nakasar ido ya kasance yana da ƴancin fita ba tare da fargaba ba.
Hikimar raba sandunan
Ya ce wasu za su yi mamakin hikimar raba sandunan, yana mai cewa yawancin sandunan da ake amfani da su ba waɗanɗa suka kamata a yi amfani da su ba ne.
"Sannan ba su da ƙwarewa ko fahimtar yada ake amfani da sandar kuma wanda za a raba musu yanzu na musamman ce da aka ƙirƙira domin ta taimaka wa makafi ko waɗanɗa ba sa gani sosai wajen tafiya."
Salisu Ibrahim yana mai cewa kafin a fitar da wannan shirin sai da suka yi bincike tare da gano manyan matsaloli kamar uku da masu larurar gani ke fama da shi.
"Na farko akasari ba sa iya amfani da sandunan zamani saboda tsadar su, sannan abu na biyu ba su da ilimin sanin yadda ake sarafata ko amfani da sandar, na uku kuma shi ne jin kunyar amfani da sandar."
Wadannan dalilai ne suka sanya aka ƙirƙiro shirin wayar da kawuna ta hanyar haɗa-kai da hukumomin kula da hanyoyi da ƙungiyoyin direbobi da malaman makarantu da ke koyar da amfani da sanduna da daliban makarantu da iyaye, sannan aka tsara littafin koyar da amfani da sanduna, in ji Salisu.
A cewarsa, sandunan kala biyu ne akwai na rukunin wanɗanda ba sa gani baki ɗaya, akwai kuma na masu gani garara-garara.
Sannan ya ce ana iya naɗe ta ko lanƙwasa sandar a jefa ta a cikin jaka ko aljihu duk lokacin da ba a bukatarta, sanduna ne na musamman da aka yi su domin daɗin tafiye-tafiye.
Yaushe za a soma rabon sandunan?
Salisu ya ce sun soma rabon sanduna a makarantu makafi da makarantu da ke da makafi cikin ɗalibansu a Kaduna.
Amma dai nan da wata biyu za a ƙaddamar da gagarumin shirin raba sanduna a wasu jihohin Najeriya
Rukunin mutanen da za su ci gajiyar sanduna sun haɗa da wadanda basa gani da marasa hali da kuma malamai da ke koyar da amfani da sanduna kuma a kyauta za a raba musu.







