Oscars 2021: Nomadland, Hopkins da Kaluuya sun lashe gasar Oscars

Asalin hoton, Reuters
Wasan kwaikwayo mai suna Nomadland ya yi nasara a rukuni uku na gasatt Oscars ciki har da matsayi na daya a fannin fitattun hotuna , yayin da fitattun taurarin fina-finan Birtaniya Sir Anthony Hopkins da Daniel Kaluuya suna lashe kyautar gwarazan taurari.
Daraktar Nomadland Chloe Zhao ta kafa tarihin zama mace ta farko da ba baturiya ba da ta lashe kyautar gwarzuar mai bayar da umarni.
Sir Anthony, mai shekara 83, shi ne mutumin da ya fi yawan shekaru da ya lashe gasar gwarzon tauraro, yayin da Kaluuya ya kasance dan wasan kwaikwayon Birtaniya bakar fata na farko da ya yi nasara a gasar Oscar - a bangaren taimaka wa babban tauraro.
'Yar fim din Birtaniya wadda ta zama mai rubuta labari da bayar da umarni Emerald Fennell ta zo ta daya a fannin rubuta wasan kwaikwayo.
Ta yi nasara a kan rubuta kirkirarren wasan kwaikwayo da fim din Promising Young Woman, wanda kuma ita ce ta bayar da umarni.
Frances McDormand ta lashe kyautar gwarzuwar tauraruwa saboda rawar da ta taka a fim din Nomadland, yayin da fitacciyar tauraruwar fina-finan Koriya ta Kudu Yuh-Jung Youn ta lashe kyautar gwarzuwa a fannin mai taimaka wa taurari a fim din Minari.
An bayar da kyautukan ne a a dakin taro na Union Station da ke birnin Los Angeles na Amurka, yayin da a bangagare daya aka bai wa taurari mazauna nasu kyautukan a wani dakin taro da ke birnin London - kodayake Sir Anthony bai halarci kowanne daga cikin bukukuwan ba
Sir Anthony ya doke Boseman

Asalin hoton, SEAN GLEASON
Sir Anthony ya lashe kyautar gwarzon tauraro saboda rawar da ya taka a matsayin mai fama da cutar mantuwa a fim din The Father, shekara 29 bayan ya lashe kyautar Oscar ta farko a fim din The Silence of the Lambs.
Nasarar da ya yi ta yi matukar bayar da mamaki. An sa ran marigayi Chadwick Boseman, wanda ya mutu yana da shekaru 43 a watan Agustan da ya gabata ne zai lashe kyautar saboda rawar da ya taka a fim Black Bottom na Ma Rainey.
Watakila shi kansa Sir Anthony ya yi mamakin lashe kyautar, shi ya sa bai halarci bkin da aka gudanar a Los Angeles da kuma wanda aka yi a dakin taro na British Film Institute a London ba.
Daren da Nomadland ya ja hankali

Asalin hoton, Reuters
Wasan kwaikwaiyon da aka gudanar kan wata mata da take rayuwa a cikin motar a-kori-kura a Amurka bayan tabarbarewar tattalin arziki shi ne ya lashe kyautar gwarzon fim, da ta gwarzon darakta da kuma gwarzuwar tauraruwa.
McDormand, wanda yanzu yake da gwarazan taurari uku na Oscars, na daya daga cikin kwararrun masu taka rawa a fim din.
Da take jawabin godiya, Zhao ta jinjina wa wadanda a zarihi suke rayuwa irin ta fulani "saboda sun koya masa yadda ake jajircewa da kuma fata".
Kafin Zhao, mace daya tilo da ta lashe kyauta a bangaren bayar da umarni a shekaru 92 da aka kwashe ana yin bikin Oscars ita ce Kathryn Bigelow a kan fim din The Hurt Locker a 2010.
Manyan fina-finan da suka lashe kyautar
- Nomadland - 3
- The Father - 2
- Judas and the Black Messiah - 2
- Ma Rainey's Black Bottom - 2
- Mank - 2
- Soul - 2
- Sound of Metal - 2
Kaluuya 'baki har kunne'

Asalin hoton, AMPAS/Reuters
Tauraron fim da ke birnin London mai shekara 32 ya lashe kyautar tauraron da ke taimaka wa babban tauraro saboda rawar da ya taka a matsayin shugaban Black Panthers Fred Hampton a Judas da kuma the Black Messiah.
Ya bayyana cewa "Ina matukar godiya da aka zabe ni domin taka rawa a matsayin mutumin da nake matukar girmama akidarsa da kuma sanya n a hanya wajen gudanar da irin rayuwarsa."
Kazalika Kaluuya ya gode wa mahaifiyarsa, wacce ke kallon bikin a BFI, wadda ya ce "ta zama silar kasancewata a wannan matsayi".






