KASU: Gwamnatin Kaduna ta yi ƙarin kuɗin makaranta ga ɗaliban Jami'ar jihar

Asalin hoton, @Kadunastatevarsity
Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da ƙarin kuɗin makaranta ga ɗaliban Jami'ar jihar ta KASU.
Kwamishinan Ilimi na jihar Dr Shehu Usman wanda ya tabbatar wa BBC da matakin, ya ce an yi ƙarin ne kudin makarantar Jami'ar ne kamar yadda aka yi ƙarin a sauran makarantun gaba da sakandare na jihar.
"An yi karin kudin makaranta a jami'ar. Wanda zai yi sabuwar rijista zai biya N150,000 wanda yake ɗan jiha," in ji shi.
Sai dai ya ce akwai bambanci kuɗi ga waɗanda ba ƴan asalin jiha ba da kuma bambanci ga wanda yake karatun ilimin fasaha da na likitanci.
Ya ce haƙƙin jami'a ne ta diba ta ga yadda za ta daidaita kuɗaɗen ga wanda zai yi sabuwar rijista da kuma kuɗin da sauran tsoffin ɗalibai za su biya.
Kwamishinan Ilimin ya ce gwamnatin ta yi ƙarin ne domin inganta karatun da kuma biyan bukatun jami'ar.
Batun ƙarin kudin makarantar jami'ar ta Kaduna ya ja hankali a shafukan sada zumunta musamman a Twitter.
Jami'ar na cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a shafin Twitter a ranar Litinin inda kusan mutum 14,000 suka yi tsokaci akai.
Wasu alƙalumma da ke yawo a kafofin sadarwa sun nuna ƙarin ya shafi ƴan asalin jihar Kaduna amma ya fi shafar waɗanda ba ƴan asalin jihar ba.
An wallafa Alƙalumman kuɗin makarantar a wani shafin Twitter da aka yi iƙirarin cewa na ɗaliban Jami'ar KASU ne. Alƙalumman sun nuna ɗaliban ɓangaren nazarin aikin likita da ba ƴan asalin jiha ba za su biya N500,000 daga N36,150 da suka saba biya na kuɗin makarantar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1
Sai dai duk da ba ta musanta rahotannin yin ƙarin ba amma jami'ar ta ƙaryata ƙayyade ƙarin kuɗaɗen da ake yaɗa wa.
Cikin wata sanarwa da jami'ar ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce duk da ana duba ƙarin kudin makarantar kan ko kowane kwas amma har yanzu ba a sanar da matakin ba. "Alkalumman da ake yaɗa wa a kafofin sada zumunta ƙarya ne," in ji sanarwar.
Alƙalumman da ake yaɗawa dai sun ce yan asalin jihar Kaduna a ɓangaren nazarin aikin likita za su biya N300,000 maimakon N26,150 da suka saba biya. Ƙarin kuma a cewar rahotannin ya shafi sauran ɓangarorin jami'ar da suka ƙunshi sashen nazarin fasaha da kimiya da ilimi.
Abin da ƴan Twitter ke cewa
Galibi ƴan Najeriya musamman a Twitter na sukar matakin ƙarin kuɗin duk da jami'ar ta musanta alƙalumman da ake yaɗawa a kafofin sadarwa na intanet.
@SarahOzuem ta ce: ƙarin kuɗin makaranta da jami'o'i ke yi mataki ne mai ban tsoro idan muka kalli batun Jami'ar Jihar Kaduna. Me zai faru ga talakawa da ba za su iya biyan kuɗin ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2
@Prodr3amer ya ce: dole yanzu mutum ya nemi tallafi kafin ya shiga jami'ar jihar Kaduna
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3
A cewar @iamthelegal kamata ya yi a ce an dakatar da ɗaukar waɗanda ba ƴan jihar Kaduna maimakon wannan ƙarin.
@_victorokonkwo kuma ya ce yana fatan wani daga Jami'ar Jihar Kaduna zai fito ya ce ƙarin da aka yi kuskure ne
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Twitter, 4
Me gwamnatin Kaduna ta ce

Asalin hoton, @govkaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ilimin firamare da sakandare shi ne ta yi alƙawalin za ta bayar kyauta.
Kwamishinan Ilimin jihar ya ce duk wani ilimi da yake gaba da firamare da sakadanre ba zai kasance kyauta ba.
Ya ce tun 2005 Jami'ar Kaduna ta so ta fara karɓar N65,000 na kudin makaranta amma a cewarsa gwamnati a wancan zamani ta amince ta riƙa karɓar N26,000, kan za ta ci gaba da cika masu sauran.
"Abin da Jami'ar ta ke karɓa daga kudin makaranta a hannun ɗalibai idan an tattara ba zai iya biyan albashin wata biyu ba."
"Gwamnati ta diba ta ga idan ta ci gaba da tafiya haka za a kai lokacin da ba za ta iya biyan albashin malamai da gudanar da dakunan bincike ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta yi ƙarin ne bayan ta diba ta ga cewa tana ba ɗalibai tallafi na karatu.
A cewar kwamishinan "wajibi ne a tabbatarwa mutane cewa arha ba ta ado - an yi hakan ne domin tabbatar da ingancin ilimi ya ƙaru."
Wasu dai na ganin karatun zai iya gagarar ƴaƴan talakawa domin dalilin kafa Jami'ar jihar don don ci gaban iliminsu.