Bill and Melinda Gates: Attajiran biyu sun kashe aurensu bayan shekaru 27 suna tare

Melinda and Bill Gates

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ma'auranta sun dauki wannan hoton ne a 2018 lokacin da suke bayanan bilyoyin kudade da suka kashe a fanin agaji

Bill da Melinda Gates sun sanar da mutuwar aurensu bayan shekaru 27 suna tare, suna mai cewa "mun fahimci ba za mu iya ci gaba da rayuwa tare a matsayin ma'aurata ba".

"Bayan nazari mai zurfi da ƙoƙarin daidaita zamanmu, mun yanke shawarar kawo karshen aurenmu," a cewar sakon da attajiran biyu suka wallafa a shafin Tuwita.

Sun hadu ne a shekarun 1980 lokacin da Melinda ta soma aiki a kamfanin Microsoft mallakin Bill.

Suna da 'ya'ya uku kuma tare suke tafiyar da Gidauniyar Bill da Melinda Gates.

Gidauniyar ta kashe biliyoyin daloli wajen yaƙi da cutuka da karfafa rigakafi ga yara.

Gidauniyar - da mai zuba jari Warren Buffett - ta samar da wani tsarin tallafi, da ke kira ga attajirai su mayar da hankali wajen fitar da kaso mai yawa na arzikinsu a fannin ayyukan ci gaba.

Bill Gates shi ne mutum na hudu mafi arziki a duniya, a cewar mujallar Forbes, ya mallaki $124bn (£89bn).

Ya samu kuɗaɗensa ne ta hanyar kamfanin Microsoft a 1970, kamfanin manhaja mafi girma a duniya.

Sakon mutanen biyu a shafinsu na Tuwita kan rabuwar yana kunshe da wasu bayanai.

"Sama da shekaru 27 na auratayarmu, mun haifa da tarbiyar da yara uku da kafa gidauniyar da ke aiki a ko ina a duniya domin taimaka wa mutane samun ingantacciyar lafiya, da rayuwa mai inganci," a cewarsu.

"Mun amince cewa za mu ci gaba da aiki tare domin cimma muradanmu da ayyukan gidauniyarmu, amma mun yarda cewa ba za mu iya ci gaba da rayuwa tare a matsayin ma'aurata ba.

"Mun nemi saukakawa juna saboda iyalinmu yayin da muke shirin soma sabon babi a rayuwarmu."

bil

Asalin hoton, others

Ya haduwar su ta kasance?

Melinda ta soma aiki a Microsoft a matsayin manaja a 1987, kuma a wannan shekarar mutanen biyu suka zauna domin tattaunawa a liyafar cin abinci a New York.

Daga nan soyayya ta shiga tsakani, amma kamar yada Bill ya shaida wa wani shirin Netflix: "Mun damu da juna sosai kuma sai ya kasance mun shiga wani yanayi na zabi biyu: wato, ko mu rabu ko mu yi aure."

Melinda ta ce ta tsinci Bill - cikin wani yanayi na tababa a zuciyarsa - yana nazari da rubuce-rubuce kan alfanu da rashin alfanun yin aure".

Sun yi aure a 1994 a tsibirin Hawaiian da ke Lanai, rahotanni na cewa sun yi hayar dukkanin jirage helikwafta domin hana bakin da ba a gayyata ba isa gare su.

Bill Gates ya bayar mukaminsa na Microsoft a shekarar da ta gabata domin mayar da hankalin kan ayyukansa na agaji.