Manyan hafsoshin tsaro da 'yan Majalisar Dattijan Najeriya sun gana kan rashin tsaro

Asalin hoton, TWITTER/@TopeBrown
Shugabannin tsaron Najeriya da na 'yan Majalisar Dattijan Najeriya sun yi wata tattaunawar sirri a zauren majalisar dokokin kasar da ke Abuja.
Hafsoshin tsaron sun amsa gayyatar 'yan majalisar ce domin bayyana musu halin da ake ciki game da taɓarɓarewar tsaro a faɗin ƙasar.
Daga ƴan majalisar har shugabannin tsaron ba su ba da cikakken bayani kan abubuwan da suka tattauna ba amma a wani saƙo da majalisar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce sun tattauna ne kan batutuwan tsaro da suka haɗa da fashin daji da ta da ƙayar baya da ta'addanci da kuma hanyoyin kawo ƙarshensu a Najeriya
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Twitter
Sai dai Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin da ke kula da harkokin soji a majalisar ya bayyana wa BBC cewa wannan ce tattaunawa mafi armashi da Majalisar Dattawan ta taɓa yi da shugabannin tsaro a Najeriya.
"Wannan tattaunawa ta yi armashi kuma mun fahimci juna sosai da shugabannin tsaron," a cewarsa.
"Za mu ba da goyon baya a ba su dukkan abun da suke buƙata don su kawo ƙarshen waɗannan matsalolin tsaro," in ji Ndume.
Sai dai ya ce ba zai bayyana ainihin abin da suka tattauna ba saboda sirri ne, ya ce akwai batutuwan da ba za a iya ambatowa ba.
Ya kuma ce majalisar ta gamsu da bayanan da shugabannin tsaron suka yi masu kuma za su taimaka masu da abubuwan da suke buƙata.
Sanata Ndume ya ce akwai abubuwan da shugabannin tsaron suka bayyana wa majalisa da ba su taɓa sani ba dagane da matsalar tsaro a Najeriya.
"Bayanan sirri ne da ba zan iya faɗa ba amma a wannan tattaunawa mun yi masu tambayoyin da ba mu taɓa yi masu ba, kuma su ma sun ba mu amsoshin da ba mu sani ba," in ji Ndume.
Ali Ndume ya ce mataki na gaba da za ɗauka shi ne duba ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi sannan a ware wa shugabannin tsaro kuɗin da suke buƙata don yin aiki yadda ya kamata.
Sauran jami'an da ke amsa gayyatar sun haɗa da da shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA da kuma na shugaban hukumar tsaron farin kaya wato DSS.
Bayan Sanata Ahmad Lawan ya gode musu bisa ayyukan kare tsaron ƙasa a madadin majalisar sai suka shiga tattaunawar sirri da misalin ƙarfe 11:21.
Suna wannan ganawa ne a yayin da Najeriya take ci gaba da fama da matsalolin tsaro daga kowacce kusurwa ta ƙasar.
A arewa maso yammacin kasar ana ci gaba da fama da matsalolin masu garkuwa da mutane da 'yan fashin daji, wadanda suke kashe mutane ko kuma su tilasta musu biyan kudin fansa.
Wannan matsala ta fi ƙamari a jihohin Kaduna da Zamfara da Neja da kuma Katsina.
Alƙaluma sun nuna cewa an sace ɗalibai fiye da 800 daga watan Disamba zuwa yanzu.
Buhari ya gaza?

Asalin hoton, Twitter/@Bashirahmaad
A baya-bayan nan, rahotanni sun nuna cewa sojoji fiye da 30 ne suka mutu sakamakon harin na mayakan Boko Haram da farmaki bisa kuskure da sojin sama suka kai a sansaninsu da ke Mainok a jihar Borno.
Sai kuma tashe-tashen hankalin da ke ci gaba da ta'azzara a kudu maso gabashin Najeriya, wanda ake zargin masu fafutukar ɓalllewa daga kasar na kungiyar IPOB ne suke kitsa su.
Hukumomi sun zarge su da kai hare-haren kan ofisoshin 'yan sanda da kubutar da daurarrun da ke gidajen yari a jihar Imo da ma wasu jihohi na yankin.
Wadannan kalubalen tsaro na cikin dalilan da suka sanya mutane da dama suke ganin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gaza inda wasu ke kira a gare shi da ya sauka daga mulki.
Sai dai shugaban kasar ya dage cewa yana yin bakin kokarinsa, yana mai cewa nan ba da jimawa ba za su shawo kan lamarin.
A farkon makon nan fadar shugaban kasar ta yi zargin cewa wasu malaman addini da tsoffin masu rike da mukamai na siyasa na son jefa kasar cikin rikici domin su yi amfani da damar wajen kifar da gwamnatinsa.
Sai dai masu sharhi sun ce wannan zargi takmar neman kawar da hankulan 'yan kasar ne daga manyan kalubalen da gwamnati ta kasa magancewa.






