Bikin Karamar Sallah: Farashin kudin mota ya tashi a Najeriya

Tasha

Rahotanni daga Najeriya na cewa kudin sufuri ya karu, yayin da wasu 'yan kasar suka fara bulaguro zuwa jihohinsu na ainihi don yin shagulgulan bikin sallah.

Dama dai ba sabon abu ba ne karin farashin kudin mota a lokaci irin wannan da jama'a ke tafiya garuruwansu.

Wasu fasinjoji da BBC ta zanta da su sun bayyana takaicinsu game da ƙarin kudin motar, sai dai kungiyoyin sufurin na cewa dole ce ta sanya su daukar wannan mataki, saboda da yanayin da ake ciki

Duk lokaci na bukukuwa kamar Karamar Sallah ko Babba ko ma bikin Kirsimeti da na Ista akan samu tashin kudin mota a Najeriya, saboda yadda jama'a ke yin tafiye tafiye don ziyartar 'yan uwansu.

Latsa hoton da ke kasa don sauraren rahoton Abdou Halilou kan wannan batun:

Bayanan sautiKudin mota ya karu a Najeriya gabanin karamar salla