Hari a Kabul: Fashewar bama-bamai ta yi sanadin mutuwar fiye da mata 'yan makaranta 50

Asalin hoton, Getty Images
An soma jana'izar mutanen da suka mutu sakamakon jerin fashe-fashen bama-bamai a kusa da wata makaranta a Kabul ranar Asabar, inda yanzu aka ce sun zarta mutum 50.
Bama-baman sun tashi ne a yayin da dalibai suke fita daga ginin da lamarin ya auku. Hukumomi sun ce galibin wadanda suka mutu 'yan mata ne dalibai.
Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare-haren a Dasht-e-Barchi - yankin da masu tayar da kayar baya na mabiya Sunnah suke yawan kai wa hari.
Jami'an gwamnatin Afghanistan sun dora alhakin harin kan mayakan Taliban, sai dai kungiyar ta musanta hannu a lamarin.
Yarinyar nan da ta samu lambar yabo ta Nobel wadda kuma take gwagwarmayar ganin 'yan mata sun samu ilimi Malala Yousafzai - wacce Taliban ta harba a ka a shekarar 2012 - ta wallafa sakon Tuwita game da harin da ta bayyana a matsayin "hari mai tayar da hankali".
"Ina bayyana jajena ga iyalan mutanen da harin makarantar Kabul ya ritsa da su," in ji ta.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Twitter

Ba a san takamaiman abin da ya sa aka kai hari a makarantar ba. An kai harin ne a yayin da Amurka take shirin janye dukkan sojojinta daga kasar Afghanistan daga yanzu zuwa ranar 11 ga watan Satumba.
Mene ne ya faru ranar Asabar?
Ana ganin fashewar ta faru ne sanadin wani bam na mota da kuma bama-bamai biyu da aka dasa a yankin.
Wata da ta tsallake rijiya da baya, Zahra, ta shaida wa manema labarai cewa tana barin makaranta a lokacin da lamarin ya faru.
"Kawata ta mutu. Mintuna kadan bayan bam din farko sai wani ya sake tashi, daga nan wani ya kuma tashi. Kowa ya rika ihu sannan ga jini ko ina," in ji ta.

Asalin hoton, EPA
Ganau da dama sun bayyana yadda bama-baman uku suka tashi, yayin da wata mata, Reza, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ta ga "gawarwaki da dama jina-jina kuma cikin ɓaraguzai da hayaƙi".
"Na ga wata mata tana duba gawarwakin kuma tana kiran sunan 'yarta," a cewar Reza. "Daga nan ta ga jakar makarantar 'yarta jina-jina sai kawai ta suma da faɗi ƙasa."
Fiye da mutum 100 ne suka jikkata sanadin harin. Rahotanni daga Kabul na cewa birnin cike yake da masu sayen kayayyaki gabanin bikin sallah da ke tafe a makon gobe.
Najiba Arian, mai magana da yawun ma'aikatar ilimi, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa makarantar ta gwamnati ce wadda maza da maza suke halarta. Galibin waɗanda suka jikkata 'yan mata ne, a cewar Ms Arian.







