Thursday and Friday: Ƴan Twitter na fatan a yi azumi 30 a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Hasashen yin azumi 30 ya ja hankali tare da faranta ran wasu ƴan Najeriya musamman masu amfani da shafin sada zumunta na Twitter.
Kwamitin ganin wata na Fadar Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya buƙaci al'ummar musulmin ƙasar su fara dibon watan Shawwal a ranar Talata da ta kasance 29 ga Ramadan.
Amma kuma kwamitin ya nuna zai yi wahala a iya ganin jinjirin watan ranar Talata.
Batun ranakun hutun da za a yi idan har aka yi azumi 30 shi ne ya ja hankalin ƴan Najeriya a Twitter.
Idan har aka yi azumi 30, kai tsaye Alhamis za ta kasance ranar Sallah a matsayin 1 ga Shawwal.
Tuni dai gwamnatin Najeriya ta sanar da Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutun Sallah.
Amma ƴan Twitter na fatan Alhamis da Juma'a a matsayin ranakun hutu - ga kuma hutun ƙarshen mako, idan an zarce da azumi Laraba.
Batun hutun Alhamis da Juma'a ya kasance ɗaya daga cikin wanda aka fi tattaunawa a Najeriya a Twitter, inda mutane kusan 7,000 suka yi tsokaci akai.

Me ake cewa?
Ƴan Najeriya da dama da suka yi tsokaci a Twitter na fatan gara ma a yi azumi 30 don su more hutun kwana huɗu a jere.
Kuma yawancin waɗanda suka yi tsokaci sun haɗa har da musulmi da waɗanda ba musulmi ba da ke fatan a yi azumi 30.
A cewar @Ab_talbah ya fi son a yi azumi 30 don hutu ya faɗo Alhamis da Juma'a ga kuma hutun ƙarshen mako.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1
Jubril A Gawat @Mr_JAGs shi ma ya ce yana son a kammala azumi a ranar Laraba don gwamnatin tarayya ta ayyana Alhamis da Juma'a a matsayin ranakun hutun Sallah.
@btope_layi ya ce: Wani abin jin daɗi a wannan makon shi ne za a yi hutu a ranakun Alhamis da Juma'a.
Abimbola @bimxy ta ambaci shugaba Buhari ta ce idan har bai ayyana Alhamis da Juma'a a matsayin hutu ba za ta ji haushi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2
ADA ISIUNE @__Garfieldu ta yi tambaya ne, shin azumi Laraba zai ƙare ko sai a ga wata sannan za a tabbatar? Ni dai ina son kwanakin hutu biyu su kasance Alhamis da Juma'a.
@xyznews_com_ng shagube ya yi cewa ragwaye ne ke murnar za a yi hutu ranakun Alhamis da Juma'a.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3

Simwal Usman Jibril mamba a kwamitin ganin wata a Fadar Sarkin Musulmi Najeriya ya shaida wa BBC cewa ko an fita neman watan a ranar Talata 29 ga Ramadan yana da wahala a a iya ganinsa saboda a cewarsa ba a ma riga an haifi watan ba sai kusan karshe takwas na dare.
"Amma ranar Laraba watan zai kasance bayan faɗuwar rana na tsawon kusan minti 42 a Najeriya kuma zai kasance yana da shekaru awa 22," in ji shi.
Ya ƙara da cewa ganinsa a ranar labara zai tabbatar da an haife shi ranar Talata bayan faɗuwar rana kuma yakan tsaya har bayan sallar Isha.
Majalisar Ƙoli ta Musulmi a Najeriya, NSCIA ta ce idan har Allah ya sa an ga watan, Sarkin Musulmi zai bayar da sanarwar ayyana Laraba a matsayin 1 ga watan Shawwal.
"Amma idan ba a ga wata ba ranar Talata, to kai tsaye Alhamis za ta kasance ranar Sallah a matsayin 1 ga Shawwal," in ji sanarwar da NSCIA ta fitar a Twitter.