Ibrahim Gambari: 'Yan fashi 'sun yi yunkurin fasa gidan shugaban ma'aikatan fadar Buhari

Ibrahim Gambari

Asalin hoton, Getty Images

Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da abin da ta kira yunkurin da wasu suka yi na fasa gidan shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ranar Litinin.

A wata sanarwa da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce wasu sun yi yunkurin fasa gidan Farfesa Ibrahim Gambari da misalin karfe uku na dare.

Kauce wa Twitter
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Twitter

Gidan nasa yana kusa da fadar shugaban kasa, a cewar sanarwar.

Sai dai Garba Shehu ya ce yunkurin nasu "bai yi nasara ba."

"A kan wannan batu, 'yan sanda suna neman wanda ya yi yunkurin fasa gidan wani mai suna Maikano Abdullahi ba tare da nasara ba ranar Alhamis ta makon jiya.

"Maikano yana zaune a kan titi daya da Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, kusa da fadar Villa," a cewar Garba Shehu.

Sai dai mai magana da yawun nan shugaban kasa ya goge sakon Tuwita da ya wallafa wanda ya ce 'yan sanda suna nazari kan hoton bidiyon da na'urar sirri ta CCTV ta dauka a gidan Mr Maikano da zummar gano dan fashin da ya shiga gidan.

Wasu rahotanni daga kafafen watsa labaran Najeriya sun ce 'yan fashin sun shiga gidajen mutanen biyu inda suka kwashi kudi da wasu kayayyaki.