Hotunan abubuwan da suka faru a Afrika a wannan makon

Zababbun fitattun hotunan abubuwan da suka faru a nahiyar da sauran su:

A ranar Laraba an nuna mana wani muhimmin bangare na yadda za ka motsa jiki a Pemba dake gabar tekun kasar Mozambique.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Laraba an nuna mana wani muhimmin bangare na yadda za ka motsa jiki a Pemba dake gabar tekun kasar Mozambique.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Lahadi tauraron wasan kwallon kafa na Liverpool dan asalin kasar Masar Mo Salah yana wasa da kwallo da fuskarsa kafin fara kara wa da kungiyar wasan kwallon kafa ta West Bromwich Albion.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dan wasan tseren kasar Uganda Jacob Kiplimo nan una galabar da ya samu bayan lashe gasar tseren mita 10,000 na maza a gasar wasan motsa jiki na Golden Spike na shekarar 2021 a Jamhuriyar Czech ranar Laraba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Talata ma'aikatan kiwon lafiya suna bi gida-gida a yankin Siaya, kasar Kenya, don yi wa mutane allurar riga-kafin korona ta AstraZeneca...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A wani labarin game da cutar korona, babban Fadan kasar Afirka ta Kudu Desmond Tutu nan una farin ciki bayan da aka yi masa allurar riga-kafin a birnin Cape Town ranar Litinin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A ranar Jumma'a wasu limaman addinin Kirsita na kasar Ethiopia suna zaune a Debre Berhan.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, daga hagu, yana yi wa shugaba Paul Kagame na kasar Rwanda lale maraba a wajen liyatar cin abincin dare a fadar shugaban kasa ta Elysee ranar Litinin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dubban mutane na ninkaya a gabar ruwan Morocco zuwa kan iyakar Ceuta na Kudancin Afirka da kasar Spaniya a cikin wannan makon….

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mutane sun soma isa kan iyakar Ceuta da sanyin safiyar ranar Litinin. Was una yin ninkaya a kusa da shingen kan iyakar ya kai ga daf da gabar tekun.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Kasar Spaniya ta ce an sake mayar da kusan rabin 'yan ciranin zuwa kasar Morocco

Duka hotunan na da haƙƙin mallaka.