Rikicin Gaza da Isra'ila cikin hotuna: Kwana 11 na ɓarnar da yaƙi ya haifar

A combination picture shows a tower building in Gaza City on May 12, 2021 (L and C) and after it was destroyed by Israeli air strikes amid a flare-up of Israeli-Palestinian violence, May 13, 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wani dogon bene a birnin Gaza (a hagu da kuma tsakiya) da yadda ya kasance bayan da Isra'ila ta kai ma sa hari ta sama (dama)

Bayan kwana 11 na yaƙi, Isra'ila da ƙungiyar Hamas ta Falasdinu sun amince su tsagaita wuta.

A kalla mutum 243 ciki har da mata da kananan yara fiye da 100 aka kashe a Gaza. A Israel kuwa, mutum 12 gwamnatin kasar ta ce an kashe ciki har da yara kanana biyu.

Kowane bangare na cewa shi ya yi nasara, amma hotunan irin barnar da su ka yi wa juna sun fara bayyana.

Please refresh your browser

Dakarun Isra'ila na cewa Hamas ta harba roka fiye da 4,300 zuwa wurare a cikin kasarta, ita kuma ta kai hari fiye da sau 1,000 a Gaza.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wani mutum na duba arnar da wani rokan da Hamas ta harba ya yi wa gidansa da ke kudancin Isra'ila

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Yadda wutar wani roka ta yi raga-raga da wani shago da motar da ke gabansa a Ramat Gan da ke wajen Tel Aviv

Fiaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya ce kasarsa ta dauki matakai masu tsanani domin kaucewa halak mutanen Gaza, yana cewa wannan matakin babu wata ƙasa a duniya da ta taɓa yin haka.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Falasɗinawa na yawo bisa wani titi da ke cikin birnin Gaza gabanin ɓarkewar wannan faɗan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ga yadda titin ya kasance bayan an tsagaita da wuta

Amma babban jami'in gwamnatin Hamas Isma'il Haniya ya ce wannan rikicin na baya-baya nan ya kori dukkan damar da ake da ita na tattaunawar zaman lafiya da kasashen biyu ke yi da juna.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tarin mutum-mutumin da aka daidaita a gaban wani shago da harin Isra'ila ya ragargaza a Gaza

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Yadda aka ruguza dogon ginin al Jalaa na birnin Gaza bayan wani harin da Isra'ila ta kai ta sama

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wani ɗan ƙasar Isra'ila na duba sauran abin da ya rage na gidansa a Sderot bayan da wani roka ya dagargaza shi da a ka harbo daga Gaza.

Asalin hoton, MAXAR TECHNOLOGIES

Bayanan hoto,

Wani babban tankin tara man fetur ke nana ke ci da wuta bayan da wani roka da aka harbo daga Gaza ya faɗa kansa

Shugabannin kasa-da-kasa na maraba da wannan tsagaita wutar da aka yi, wanda Masar ta shiga tsakani har aka same shi.

.