Amurka za ta taimaka a sake gina Gaza

Yara a cikin rushasshen gidansu

Asalin hoton, EEFP

Bayanan hoto,

Daruruwan gidajen Falasdinawa hare-haren makamai masu linzami suka lalata a Gaza.

Shugaba Amurka Joe Biden ya yi alkawarin taimakawa wajen sake gina zirin Gaza a daidai lokacin da Falasdinawa ke bayyana irin barnar da hare-haren makamai masu linzami da Isra'ila ta dinga kai wa yankin a kwanaki 11 da aka dauka ana gwabzawa a tsakaninsu.

Daruruwan gidaje aka dalalata, kuma jami'an Falasdinawa sun ce ana bukatar gwamman miliyoyin dalolin wajen sake gina su.

A jiya Juma'a ayarin motocin agaji na farko suka isa yankin Falasdinawa. Shugaba Biden ya ce matukar ana son cimma nasarar kawo karshen rikicin, dole dukkan bangarorin biyu sun amince da hakan.

Sannan ya bayyana karara tsarinsa ya sha banban da na wanda ya gada shugaba, Donald Trump musamman kan manufar gwamnatinsa ga sauran kasashe. Wasu 'yan jam'iyyar Democrats dai sun bukaci Mr Biden ya dauki tsattsauran mataki kan Isra'ila.

An cimma yarjejeniyar dakatar da budewa wuta, wadda Masar ta shiga tsakani da ta fara aiki a ranar Juma'a. Sai dai da yammacin ranar aka sake taho mu gama tsakanin sojojin Isra'ila da Falasdinawa a masallacin Kudus.

Sama da mutane 250 rikicin ya hallaka, kuma kashi 90 cikin 100 Falasdinawa mata da kananan yara ne. Rabon da Isra'ila ta kai irin wadannan hare-haren yankin Falasdinawa tun a shekarar 2015.