Mutumin da ya kai wa Limamin Ka'aba hari ya ce shi "Mahdi ne"

Sheikh Baleelah lokacin da yake gabatar da huɗubar Sallar Juma'a.

Asalin hoton, @hsharifain

Bayanan hoto,

Mutumin ya yi yunkurin halaka Sheikh Baleelah lokacin da yake gabatar da huɗubar Sallar Juma'a.

Mutumin da ya kai wa Limamin Masallacin Ka'aba hari a Juma'a 21 ga watan Mayun 2021 ya ce shi "Mahadi ne"

Hukumomin da ke kula da Masallatai biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain sun ce mutumin ya yi yunƙurin halaka Sheikh Bandar Baleelah ne lokacin da yake gabatar da huɗubar Sallar Juma'a.

Haramain Sharifain ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata 25 ga watan Mayu cewa, mutumin wanda ɗan ƙasar Saudiyyan ne mai shekara 40, ya yi ikirarin cewa shi Imamu Mahdi ne.

Ya faɗi hakan ne a yayin da ƴan sanda suke tuhumarsa. Sai dai hukumar ba ta yi ƙarin bayani kan matakin da aka ɗauka a kansa ba.

Mutumin ya yi ƙoƙarin aikata wannan aika-aikar ne a yayin da yake sanye da harami a jikinsa.

Imamu Mahadi shi ne wani mutum da wasu Musulmai suka yi imanin cewa zai zo a ƙarshen duniya.

Haramain Sharifain ya wallafa bidiyon a shafukansa na sada zumunsa yadda mutumin ya yi yunƙurin kutsawa ga limamin da kuma yadda jami'an tsaro suka murƙushe shi.

Hukumomin sun ce "mutumin ya tunkari mumbarin limamin ne riƙe da makami a masallacin Ka'aba amma an yi nasarar murƙushe shi."

An taɓa yunƙurin kutsawa da mota cikin Masallacin Ka'aba a guje

An taɓa yunƙurin kutsawa da wata mota cikin Masallacin Ka'aba a guje, inda ta dangane da ƙofar shiga cikin masallacin ta 89.

Lamarin ya faru ne a watan Oktoban 2020 a daren juma'a

Motar ta kunna kai ta Farfajiyar Sarki Fahd, wadda aka haɗe ta da masallacin daga baya.

Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta ya nuna yadda motar ta yi awon gaba da shingen kariya sannan ta dangane da ƙofar shiga masallacin.

Sai dai hukumomi sun bayyana cewa babu wanda ya jikkata a hatsarin sannan kuma an kama direban nan take. Wasu hotuna sun nuna yadda aka ɗaure hannayensa kafin a fita da shi.