Yadda aka yi jana'izar Janar Attahiru da sojojin Najeriya 10

Yadda aka yi jana'izar Janar Attahiru da sojojin Najeriya 10

An binne gawar Babban Hafsan Sojan Ƙasa na Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru tare da sauran sojoji 10 da suka rasu a Maƙabarta ta Ƙasa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

Mutum shida aka yi wa sallah a masallacin Abuja daga cikin 11 da hatsarin jirgin saman ya yi ajalinsu.

An yi wa Kiristoci biyar daga cikinsu tasu jana'izar a Babbar Cocin Ƙasa da ke Abujar.