Janar Ibrahim Attahiru: Yadda aka yi jana'izar sojojin Najeriya 11 da suka mutu a hatsarin jirgi

Bayanan bidiyo,

Latsa hoton sama ku kalli yadda sojoji suka binne sojojin Najeriya 11

A ranar Asabar, 22 ga watan Mayun 2021 aka binne gawar Babban Hafsan Sojan Ƙasa na Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru tare da sauran sojoji 10 da suka rasu a Maƙabarta ta Ƙasa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

Mutum shida aka yi wa sallah a masallacin Abuja daga cikin 11 da hatsarin jirgin saman ya yi ajalinsu.

An yi wa Kiristoci biyar daga cikinsu tasu jana'izar a Babbar Cocin Ƙasa da ke Abujar.

Manyan jami'an gwamnati ne suka halarci jana'izar da suka ƙunshi shugaban Majalisar Dattawa da babban sufeton ƴan sanda da ministan sadarwa da shugaban jam'iyyar APC mai mulki da sauransu.

Yadda hatsarin jirgin ya faru

Asalin hoton, Nigeria Airforce

Manyan sojojin na Najeriya sun rasu ne sakamakon hatsarin da jirginsu na soja ya yi a Jihar Kaduna.

Bayanai sun ce jirgin saman na soji ya fadi ne a kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Kaduna kuma mutum takwas ne a cikin jirgin lokacin da lamarin ya faru.

Duk da cewa hukumomi ba su tabbatar da musabbabin hatsarin ba, wasu rahotanni na cewa akwai yanayi maras a jihar lokacin da jirgin ya faɗo ƙasa.

Tun farko rundunar sojin saman Najeriyar ta wallafa wani saƙo a shafinta na Twiiter inda ta bayyana cewa wani jirginta ya faɗi a kusa da filin jirgin sama na Kaduna.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, rundunar ta ce tana bincike kan abin da ya haifar da hatsarin.

Sunayen sojojin da suka rasu a hatsarin

Jaridar Daily Trust ta bayyana sunayensu kamar haka:

 • Laftanar Janar Ibrahim Attahiru
 • Birgediya Janar MI Abdulkadir
 • Birgediya Janar Olayinka
 • Birgediya Janar Abdurrahman Kuliya
 • Manjo LA Hayat
 • Manjo Hamza
 • Saja Umar
 • Matuƙin Jirgi TO Asaniyi
 • Matuƙin Jirgi AA Olufade
 • Saja Adesina
 • ACM Oyedepo

Wane ne Janar Attahiru?

Asalin hoton, Nigerian Army

Marigayi Laftanar Janar Attahiru Ibrahim ya zama Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Najeriya a watan Janairun 2021.

Kafin mutuwarsa, Janar Attahiru Ibrahim ne ke jagotrantar yaki da masu tayar da kayar baya a Najeriya.

An haifi marigayi Attahiru Ibrahim ranar 10 ga watan Agustan 1966.

Ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa ne ta jihar Kaduna, kuma ya halarci makarantar horas da hafsoshin soji ta Nigerian Defence Academy da ke Kaduna, inda ya zama cikin ajin hafsoshin da suka halarci kwalejin na 35.

Marigayin ya kammala karatunsa a kwalejin da aka fi sani da NDA, da kuma Armed Forces Command Staff College, da ke Jaji har ma da kwalejin da ke horas da ƙananan hafsoshin sojin kasa mai suna Nigerian Army school of Infantry dukkansu a jihar Kaduna.

An fara horas da shi ne a NDA a watan Janairun 1984, inda ya fito da mukamin Second Lieutenant a watan Disambar 1986 a matsayin cikakken hafsan sojan Infantry wato na ƙasa.