Obi Cubana: Jana'izar alfarmar da ta jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya

Obinna Iyiegbu shi ne mai kamfanin gidajen cin abinci da harkokin nishadantarwa a Najeriya

Asalin hoton, OBI CUBANA/INSTAGRAM

Bayanan hoto,

Obinna Iyiegbu shi ne mai kamfanin gidajen cin abinci da harkokin nishadantarwa a Najeriya

Obinna Iyiegbu, wanda mutane suka fi sani da Obi Cubana, ya yi bayanai a wata tattaunawa ta musamman kan rayuwarsa da kuma yadda ya taso.

Ɗan kasuwar mai shekara 46, daga yankin gabashin Najeriya wanda ke gudanar da harkokin kasuwancin nishadantarwa da karramawa, daga mahaifarsa ta yankin Idemili ta Kudu, Obi Cubana ya zauna don tattaunawa a kan abubuwa da dama da suka hada da yadda ya fara gudanar da harkar kasuwancinsa.

Shahararren ɗan kasuwar wanda ya yi bikin binne mahaifiyarsa a garinsa na Oba a cikin karshen mako daga ranakun 16 da 17 da kuma 18 ga watan Yulin shekarar 2021, ya zama wani babban labari a shafukan intanet, inda ya yi magana a kan rawar da iyayensa suka taka wajen karatunsa, da kuma yadda ya fara samun Naira miliyan ɗaya kwatankwacin dala dubu biyu da dari hudu ($2,400).

Oba gari ne da babu hayaniya mai kauyuka tara, da ke tsakanin garin Onitsha cibiyar kasuwancin yankin da kuma garin Nnewi mai masana'antu.

Lokacin yakin basasa, nan ne babbar cibiyar sojojin Biafra. Amma yanzu za a daɗe ana tunawa da wannan yanki saboda bikin binne mahaifiyar Obi Cubana

Bikin Binnewar

A cikin karshen mako daga ranakun 16, da 17, da 18 ga watan Yulin sekarar 2021, bikin binne mahaifiyar Obi Cubana, wanda ya gudanar a garinsu na Oba, ya zama babban labari a shafukan sada zumunta kan ko me yasa.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Labari ya bazu cewa zuwa ranar Jumma'a Obi Cubana zai gudanar da abubuwan tunawa ga mahaifiyarsa da sarkar wuya da kwadon sarka da darajarsu ta kai dala dubu dari $100,000 da kuma kashe kudin da suka zarta haka wajen bikin binneta.

“Hakan ya faru ne saboda mun yi wa mahaifiyarmu alkawarin cewa a duk lokacin da ta cika shekara 80 da haihuwa, irin bukukuwan da babu wanda ya taba yi a duniya,'' Obi ya bayyana dalilan da suka saka bikin binnewar ya zama babban labari.

Amma kuma in ji shi, a lokacin da mahaifiyarsu ta rasu kafin ta cika shekara 80, sai suka yanke shawarar karkatar da duka tsare-tsare da sauran abubuwa zuwa lokacin bikin binnewar.

Naira miliyan ɗaya ta farko da ya samu

Obi wanda ya kammala karatun jami'a a fannin kimiyyar siyasa ya ce bayan da ya kammala makarantar, ya yi aikin yi wa kasa hidima (NYSC) a Abuja cikin shekarar 1999 inda ya yi aiki a Majalisar Dokoki.

A lokaci guda kuma Obi Cubana ya shiga harkar kasuwancin dillancin gidaje, yana sayar da filaye da kuma rukunan gidaje.

“Daga nan ne na fara jin kamshin 5 bisa dari a rayuwata!”

Amma wani babban abu kuma shi ne, yayin da na samu wani mutum da ya ba ni kwangilar gyaran gida.

“Mun yi aiki mai kyau, ya ba ni naira dubu ɗari biyar....a cikin aikin da ribata ita ce naira dubu ɗari shida da kaɗan, don haka na sami naira miliyan ɗaya da dubu ɗari ke nan.''

Daga baya sauran ayyuka suka rika biyo baya.

“Na riƙa yin kananan kwangiloli wa kamfanin mai na kasa PPMC, ina samun ƴan kuɗaɗe a lokacin kuma na sayi motar Marsandi samfurin V-Boot, ta hakan ne muka fara rayuwa.''

Mahaifiya da kuma Mahaifi

Hamshakin ɗan kasuwar ya yaba wa iyayensa sosai kan yadda suka rene su shi da 'yanuwansa, musamman mahaifiyarsa, wacce ya ce ta kasance komai nasu tun bayan rasuwar mahaifinsa shekaru 15 da suka gabata.

“Ita ce ta zame mana uwa da kuma uba, kafin ka tafi ko ina dole sai ta yi maka addu'a,'' in ji ɗan kasuwar mazauni a birnin Lagos lokacin da yake magana a kan mahaifiyarsa.

Ya ce mahaifiyarsa ta koyar a makarantar firamaren da yake: Central School, Oba.

Liƙi da watsar da kuɗi

Asalin hoton, CUBANA CHIEF PRIEST/INSTAGRAM

Bayanan hoto,

Obi Cubana

Obi Cubana ya kare maganganun da ake yi game da liƙi da watsar da takardun kuɗin da bakin da aka gayyata suka riƙa yi, da cewa kuɗinsu ne don haka suna da damar amfani da su yadda suka ga dama.

''Ta ya ya za a ce ni na shirya yadda mutane za su riƙa watsa kuɗi, wanka zan yi dasu? Kuɗinsu ne...su suke da kuɗin da kuma irin salon rayuwarsu.

“Ba irin mutanen da zan iya juyawa ba ne in ce musu yi ko kada ku yi'....amma na ji a raina cewa kauna ce suka zo su nuna min.''

Karya doka ne a bisa dokar Babban Bannkin Najeriya (CBN), a bisa dokar watsa kuɗi saboda suna daukar haka a matsayin ''rashin mutuntawa da cin mutuncin kuɗin ƙasar' da ke tattare da haɗarin yiwuwar ɗaurin watanni da suka wuce shida a gidan yari ko kuma tarar naira dubu hamsin ko kuma duka.

'Babu wanda zai saka ka a hanya'

“Babu wanda zai saka ka a hanyar samun ci gaba a wannan duniyar!”

Obi Cubana ya bai wa mutane shawarar cewa idan suna addu'ar samun dorewar cigaba a cikin abubuwan da suka sa a gaba, su yi ƙoƙarin hada dangantaka mai kyau da mutane, za ka yi dace da samun nasara.

Ya ce cikin shekaru biyu fara yin abubuwan da ya yi magana a kai, harkokin kasuwancin mutum zai bunƙasa.

Ka yi aiki, ka yi addu'a, ka zama mai kamala, ta hakan ne za ka samu hanyarka ta kai wa ga nasara. Haka abin yake.''

Ba bikin rayuwar da mamaci ya yi ba ne, almubazzaranci ne!

A wata maƙala da wani gogaggen ɗan jarida a Najeriya Reuben Abati ya rubuta a shafin jaridar Sahara Reporters game da abinda ya bayyana almubazzaranci da kuɗi da aka yi a wurin bikin binne mahaifiyar hamshakin mai kudin Obi Cubana, ya ce babba abin takaici ne da damuwa idan aka duba halin da ƙasar ke ciki.

Ko shakka babu in ji Mista Abati an yi wasa da almubazzaranci da kuɗi a wurin bikin binnewar fiye da yadda ake tsammani.

''Faifen bidiyon farko da na kalla, na wani matashi ne na watsa takardun kuɗi ta ko ina a kan tittuna kai ka ce yana watsa wa kananan yara alawowi ne. Takardun kuɗin na cikin fakiti-fakiti, kuma ana jefa ko wane bandir na sabbin takardun kuɗi a cikin taron jama'a, mutane na faɗuwa ƙasa suna rubibi.''

Abati ya kuma bayyana cikin takaici da cewa wannan ba kirkin da ya shafi rayuwa bane. Bikin nuna kuɗi ne. Mahaifiyar Obi Cubana ta rasu tun watan Nuwambar shekarar 2020, amma sai da ya dauke shi tsawon watanni bakwai ya shirya yadda zai yi bikin binneta,'' in ji Mista Reuben.

''Kana a daidai lokacin da ya ga cewa lokaci ya yi da za a kai mai mutuwar makwancinta, aniyarsa ita ce ya shiryawa mahaifiyarsa kasaitacciyar jana'iza, irin wacce ko wadanda ke raye za su yi wa mamaci hassada tare da fatan su ma su mutu.''

Babban bakin Najeriya - Sashi na 5, in ji Mista Reuben a maƙalar ta shi, ta tanadi hukunci kan abinda ta nuna cin mutuncin takardun kudin kasa, na daurin watanni shida a gidan yari ko kuma tarar naira dubu N50,000 ko kuma duka, amma ba ta da wani tasiri.

''Wannan hukunci ba shi da tsanani, bana jin hakan zai yi wani tasiri a kan Obi Cubana ko ire-irensa, hukunci mai tsanani ya kamata ba wannan ba!,'' in ji Reuben..

''Rawar da shafukan sada zumunta suka taka, da kuma abokan Cubana ta yi kyau: yadda kasa ta rasa mutuntaka da darajarta, bayan da ta samar da sabbin 'yan zamani a Najeriya da suke bauta wa kuɗi, da kuma nuna izza da girman kai.''