Super Tucano: Abubuwan da ba ku sani ba kan jiragen yakin da Najeriya ta saya

Jirgin yaki na Super Tucano na iya gudun kilomita 590 a ko wace sa'a daya da kuma tafiyar nisan kololuwar sama ta kafa 35,000.

Asalin hoton, NIGERIA ARMY

Bayanan hoto,

Jirgin yaki na Super Tucano na iya gudun kilomita 590 a ko wace sa'a daya da kuma tafiyar nisan kololuwar sama ta kafa 35,000.

A ranar Alhamis ne rukunin farko na jiragen yakin da Najeriya ta saya samfurin A-29 Super Tucano suka isa kasar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar ta ce Ministan Tsaro Manjo Bashir Magashi (mai ritaya) ne ya karbi jiragen a jihar Kano, da rakiyar Babban Hafsan Sojin kasa Laftanar Janar Faruk Yahaya da Babban Hafsan Sojin sama Air Marshan Oladayo Amao.

Kamfanin kera jiragen sama na Embraer S.A na kasar Brazil ne ke kera samfurin jiragen na Super Tucano A-29.

A watan Disambar shekarar 2018 ne kamfanin na Embraer da abokin huddarsa na kasar Saliyo Nevada Corporation (SNC) suka samu kwangilar sayen jirage 12 na A-29 Super Tecano daga Rundunar Sojin Saman Najeriya NAF.

Kwangilar ta kuma kunshi kayayyakin horarwa daga kasa, da na'urorin tsara ayyukan soji, da sauran kayayyakin aiki ga rundunar sojin saman ta Najeriya.

Jirgin samfurin A-29 ya kammala kaddamar da tashinsa na farko ne ga rundunar ta NAF a watan Afrilun shekarar 2020.

Ana sa ran kammala kawo daukacin jiragen da Najeriyar ta saya a cikin shekarar 2021.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tun a lokacin mulkin tsohon shugaban Amurka Barack Obama ne gwamnatinsa ta bukaci amincewar sayar da jirgin yakin na Super Tucano ga Najeriya don taimaka mata wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Abubuwan da suka kamata ku sani game da jirgin

Wuri na biyu da ake kera wannan jirgi a jihar Florida ta Amurka yake, tare da hadin gwuiwa tsakanin kamfanin Nevada Corporation da kuma kamfanin na Embraer.

Ana kuma amfani da jirgin ne wajen ayyukan horar da matuka jirgin da harkokin tsaro da bincike da kuma yaki da ta'addanci.

Karfin gudu da zafin nama

Jirgin yakin Super Tucano, wanda ke da kaifin saurin tashi da gudun wuce sa'a mai amfani da karfin farfela, ana amfani da shi sosai a Afirka, da Latin Amurka da wasu kasashen.

Jirgin na iya daukar tarin makamai da suka hada da manyan bindigogi da aka riga aka saita.

Kana an saka masa kayan lataroni na zamani, da na'urorin sadarwa da sansano duk wani abu daga nesa, da zai ba shi damar yin aiki daga wurare masu nisa.

Jirgin yaki na Super Tucano na iya gudun kilomita 590 a ko wace sa'a daya da kuma tafiyar nisan kololuwar sama ta kafa 35,000.

Kirar samfurin farko na jirgin Super Tucano ya fara tashi a shekarar 1992, kuma duka samufurin biyu wato Tucano da kuma Super Tucano, kamfanin na Embraer ne ya kera su.

Baya ga horar da matuka jirgin sama a matakan farko da kuma mafi girmansa, manyan ayyukan jirgin su ne na amfani wajen ayyukan sintirin kan iyakoki da kuma yaki da ta'addanci.

Iyakar ka'idar daukar nauyi na jirgin giram 7 ne, kana kankantarsa, da kananan na'urorin hange da kuma gano hanya da nisa hade da karfin gudu da zafin nama, na kara wa jirgin karko.

Sauran abubuwan da ke kara masa karko sun hada da sulken kariya, da muhimman na'urorin shirin ko-ta-kwana.

Wurin zaman matukin jirgin

Bangaren matukin jirgin da daukacinsa gilashi ne, ya dace da wasu tabarau na kallon duhun dare.

An kuma sanya masa na'ura mai kwakwalwa daga saman kai, mai nuna wa matukin tsari da yanayin yadda jirgi ke bi.

An kuma samar wa matukin jirgin wata sanda wadda yake sarrafa jirgin.

Matukin jirgin na samun kariya daga nau'un sulken da aka daura wa damarar dafaffiyar roba a kujearar da ba za ta iya fita ba.

Akwai kuma wasu na'urori da aka dasa a gaba da kuma bayan wurin zaman matukin wadanda ke kunshe da gilasai masu jurewa karfin karo da babban tsuntsu.

An kuma saka masa na'urar samar da iskar shaka ta oxygen a cikin jirgin.

Karfin daukar makamai

Jirgin Super Tucano na da wasu bangarori biyar masu karfi wajen iya daukar makamai.

Tsarin na'urorin cikin jirgin ya kunshi manhajar sarrafa makamai, da wurin alkinta makaman, da wurin tsara kai hari da kuma yin gwaji.

Akwai gurabai biyar na daukar makamai, kuma jirgin na da karfin daukar nauyin kaya na akalla kilogiram 1,500.

Jirgin yana kuma da manyan bindigogin igwa a ko wadanne bangarori biyu na fuka-fukansa da ke da adadin harba wuta sau 1,100 a cikin minti daya kacal, kana yana iya daukar bama-bamai da kuma makamai masu linzami ta sama da kuma ta kasa.

Tsarin na'urorin jirgin kan ba shi damar lura da kuma kallon abubuwan da ke faruwa a lokacin gudanar da aiki cikin dare.

Tukin jirgin

An saka wa jirgin na'urorin tuki na zamani da na tsarin kai hari, da saita tsarin tukin, da kuma nuna nisan wurare, da kuma na'urar da ke ankarar da matuki yadda zai kauce wa yin karo.

Kasashen duniya sun yi rubibin jirgin

Kasashen duniya da dama ne ke amfani da samfurin jiragen yakin fiye da 200, kamar yadda Embraer ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Rundunonin sojin sama a fadin duniya na ci gaba da zabar yin amfani da samfurin jirgin yaki na A-29 Super Tucano, in ji kamfanin na Embraer.

Rundunonin sojin sun hada da na kasashen Afghanistan, da Angola, da Brazil, da Burkina Faso, da Chile, da Colombia, da Jamhuriyar Dominic, da Ecuador, da Indonesia da Mauritania - wadanda duka suna amfani da jirgin yakin Super Tucano.

Kana sai kasashen Guatemala, da Senegal, da Ghana, da Mali da kuma Lebanon suka yi oda daga bayan su.

A shekarar 2016 ne aka kai wa kasar Afghanistan rukunin farko na jiragen hudu cikin 20 da ta saya daga kamfanin.

Kudin sayen jirgin na Super Tucano ya kai fiye da dala miliyan 10 ko wanne, kuma farashin ka iya fin haka, saboda ya danganta da irin abubuwan da aka hada masa.

A cikin watan Agustan shekarar 2001, kamfanin Embraer ya sanar da rattaba hannun yarjejeniyar kwangila da Jamhuriyar Dominic ta kera jiragen yaki na Super Tucano goma da za ta yi amfani da su wajen ayyukan horar da matuka jirgi, da harkokin tsaron cikin gida, da sintirin kan iyakoki, da kuma yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi.

Kamfanin na Embraer ya samu sauke wa kasar ta Jamhuriyar Dominic rukunin farko na jiragen Super Tucano din biyu ranar 18 ga watan Disambar shekarar 2009.

Kana a watan Yunin shekarar 2010 ne ya sake sauke karin jiragen uku a kasar.

Har ila yau kasar Venezuela ta zabi sayen samfurin jirgin yakin na Super Tucano a watan Fabrairun shekarar 2005.

Da farko ta fara aniyar odar sayen jirage 12, tare da shirin sayen karin wasu 12.

Amma kuma cikinin bai fada ba saboda tunanin cewa Amurka za ta toshe hanyar kai jiragen da aka kera a kasar.

A watan Disambar shekarar 2005, Rundunar Sojin Saman kasar Columbia ta bayar da kwangilar sayen jiragen yakin na Super Tucano 25.

An kuma sauke musu rukunin farko na guda biyar a shekarar 2006, kana a shekarar 2008 a karasa kai musu sauran.

Ita ma Rundunar Sojin Saman kasar Chile ta zabi sayen wannan jiragen 12 a watan Afrilun shekarar 2008.

Embraer din ya kai musu rukunin farko guda hudu cikin 12 a ranar 23 ga watan Disambar shekarar 2009.

Haka ita ma Rundunar Sojin Saman kasar Ecuador ta sayi jirage 24 na Super Tucano a watan Mayun shekarar 2009 a wani bangare na yarjejeniyar kwangilar sayen ta dala miliyan 270 da suka rattaba wa hannu tare da kamafanin na Embraer a shekarar 2008.

Kamfanin ya samar masa da kashin farko na jirage shida daga cikin a watan Afrilun shekarar 2010.

Kuma a watan Disambar shekarar 2010 ne Ma'aikatar Harkokin Tsaro ta kasar Indonesia ta rattaba hannnun yarjejeniyar kwangilasr ta sayen jiragen yakin na Super Tucano A-29 takwas da kamfanin na Embraer.