Ƙayatattun hotuna daga Afirka: daga ranar 23 zuwa 29 ga watan Yuli na 2021

Wasu ƙayatattun hotuna daga sassa daban-daban na nahiyar Afirka da wajen ta:

Children holding leaves to protect themselves from the rain pose in Boffa, Guinea - Sunday 25 July 2021

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Ranar Lahadi, wasu yara na kare kansu da manyan ganye yayin da ake ruwan sama a Guinea.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A Ivory Coast mai makwabtaka da Guinea, wani yaro ne ke tallan abarba ranar Laraba a Abidjan, ɗaya daga cikin manyan biranen ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A Zirin Gaza kuwa, wani zane na Khaby Lame ake iya gani a jikin wani gini ranar Litinin. Lame, mai shekara 21, an haife shi ne a Senegal amma yana zaune ne a Italiya, kuma bidiyon barkwancin da yake haɗa wa sun sa ya zama mutum na biyu da aka fi bibiya a shafin TikTok.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Tun da aka fara gasar Olympics, ƴan wasa daga Afirka suna jan hankulan jama'a sosai, cikinsu har da dan wasan ƙwallon tennis na tebur mai suna Ibrahima Diaw ɗan kasar Senegal a ranar Asabar...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yini guda gabanin bikin buɗe gasar Olympics a Tokyo, wata ƴar wasa daga Colombia ta ɗauki hoton kanta a gaban wasu ƴan tawagar ƙasar Kenya...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ƴan Kenya na jan hankulan jama'a a gasar ta Olympics - a nan ƴan wasan rugby na ƙasar ne ke sanye da kayansu masu kyawu yayin da za su buga wasansu ranar Litinin...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A wannan yinin ne kuma ɗan wasan ƙasar Moroko Mehdi Essadiq ya shiga gasar gudu da ninƙaya...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ɗan wasan dambe na ƙasar Moroko Abdelhaq Nadir - wanda hotonsa ke sama - ya burge mutane domin zanen zobunan gasar Olympics da ya yi a hannunsa...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A ranar Alhamis, ita ma wannan ƴar wasan ninƙaya ta ƙasar Afirka ta Kudu mai suna Kaylene Corbett ta zana zobunan Olympics ɗin a ƙumbar hannunta...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ƴar wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Zambia Racheal Kundananji yayin da ta ke tka leda a wasan da ta buga yayin da Zambiya ta kara da China ranar Asabar...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shi kuwa ɗan wasan ƙwallon kwando na Najeriya Josh Okogie na ƙoƙarin jefa ƙwallo a ragar Ostreliya ranar Lahadi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A wannan ranar ce mutane su ka fita bisa titunan babban birnin ƙasar Tunisiya bayan da shugabansu ya dakatar da ayyukan majalisar kuma ya kori firaministan ƙasar bayan zanga-zangar da jama'a su ka yi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ga ƴan Ivory Coast, ganin shugabansu Alassane Ouattara (a dama) tare da wanda ya gada Laurent Gbagbo (a hagu) na riƙe hannu kuma su na dariya abu ne da tilas zai ja hankula. Tsofaffin abokan hamayyar na ƙoƙarin warkar da ciwon da ya bayyana bayan yaƙin basasan da aka yi shekara 10 da ta gabata.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kashegari a birnin Abidjan, wani matashi ya riƙa burge ƴan kallo a bisa babur ɗinsa...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A nan kuwa wasu ne ke bisa dawaki a gaɓar tekun birnin - duka a ranar Laraba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ranar Talata a birnin Addis Ababa, wata ƴar ƙasar Habasha na kallon masu zanga-zanga da ke nuna bacin ransu kan ƴan tawayen da ke yaƙi da gwamnati a Tigray...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wasu matasa na murna bayan da aka ɗauke su aikin soja domin su tafi fagen dagar yaƙin da ya ɓarke a arewacin Habasha a watan Nuwamba.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka