Bukola Saraki: Tsohon shugaban majalisar ya koma gida bayan amsa gayyatar EFC

Bukola Saraki

Asalin hoton, @bukolasaraki

Bayanan hoto,

A baya ya fuskanci shari'a bisa zargin kin bayyana kaddarorinsa amma Kotun Kolin Najeriya ta wanke shi a shekara ta 2018

Ofishin watsa labaran tsohon shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki, ya ce ɗan siyasar ya koma gidansa, bayan amsa gayyatar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar EFCC ta yi masa.

Haka nan kuma ya karyata wasu rahotanni da jaridun Najeriyar suka ce jami'an hukumar sun tsare shi bayan amsa gayyatar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin Bukola Saraki Yusuph Olaniyonu, ta ce tsohon shugaban majalisar dattawan ya tabbatar wa EFCC cewa a shirye yake ya amsa gayyatarsu a duk lokacin da suka bukaci wani karin haske daga gare shi, yana cewa "Babu wani abu da zai boye musu."

Da farko dai, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa BBC ranar Asabar cewa sun gayyaci Sanata Saraki ne domin ya amsa wasu tambayoyi game da zarge-zargen cin hanci.

Sai dai bai yi cikakken bayani kan zarge-zargen da suke yi wa tsohon gwamnan jihar ta Kwara ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bukola Saraki

Amma kafofin watsa labaran kasar sun bayyana cewa ana tuhumar Sanata Saraki ne bisa zarge-zargen sata da halasta kudin haramun.

Sanata Saraki, wanda ya shafe shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Kwara, ya daɗe yana fuskantar zargin cin hanci da kuma halatta kudin haramun.

A baya ya fuskanci shari'a bisa zargin kin bayyana kaddarorinsa amma Kotun Kolin Najeriya ta wanke shi a shekara ta 2018.

A 2019, EFCC ta garkame gidaje akalla biyar na Sanata Saraki da ke jihar Lagos bayan ta yi zargin cewa ya mallake su "ta hanyar wawure baitul malin jihar Kwara domin azurta kansa."

A lokacin da yake shugabancin majalisar dattawa, an sha kai ruwa rana tsakaninsa da na bangaren zartarwa karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.