Nnamdi Kanu: Umarnin IPOB ga jama'ar kudu maso gabashin Najeriya ya haifar da zaman zullumi

Titunan wasu biranen jihohin kudu maso gabashin Najeriya sun kasance fayau ranar Litinin
Bayanan hoto,

Titunan wasu biranen jihohin kudu maso gabashin Najeriya sun kasance fayau ranar Litinin

Ana zaman zullumi da rashin tabbas a yankin kudu maso gabashin Najeriya sakamakon umarnin da kungiyar 'yan a-ware ta IPOB ta bai wa mazauna yankin da kada su fito wuraren ayyuka da harkokinsu na kasuwanci a ranar Litinin.

Amma hukumomi a yankin sun gargadi jama'a da kada su kuskura su bi umarnin da kungiyar IPOB mai rajin ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biafra ta bayar.

IPOB ta bayar da umarnin ne don nuna rashin jin dadinta da ci gaba da tsare jagoranta Nnamdi Kanu da hukumomin kasar ke yi yayin da yake fuskantar shari'a.

Mahukunta a jihohin Abia da Anambra da Imo da kuma Ebonyi sun bukaci jama'ar yankin da su yi biris da umarnin na 'yan aware, kana su fito harkokinsa na yau da kullum kamar yadda suka saba.

Gwamnatocin jihohin sun jaddada kiran, musamman ga ma'aikatan gwamnati da 'yan kasuwa.

Wasu gwamnatocin sun ma gargadi ma'aikatansu da cewa duk wanda bai tafi wurin aiki ba, to za a rage masa albashi.

Dokta Declan Emelumba, kwamishinan watsa labarai na jihar Imo ya ce ''ranar Litinin ba ranar hutu ba ce.''

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

'Muna cikin fargaba'

Wasu mazauna jihar ta Imo sun shaida wa BBC cewa suna cikin halin rashin tabbas dangane wannan yanayi na kiki-kaka tsakanin 'yan aware da gwamnati.

Wani mazaunin jihar ya shaida wa BBC cewa babu wani tashin hankali ko tarzoma amma ''gaskiya dai muna cikin halin dardar.''

A jihar Abia kuwa, wani mazaunin garin Aba, ya ce garin ya kasance shiru kuma ana zullumi domin mutane suna fargabar abin da ka iya faruwa dangane da barazanar kungiyar IPOB.

Mazaunin garin na Aba wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce adadin baki 'yan kasuwa da kan shiga garin a kowane mako ya ragu matuka.

A cewarsa mutane dai yawanci suna ''fargaba ne a kan abin da zai iya faruwa.''

To sai dai gwamnatocin jihohin yankin na kudu maso gabashin Najeriya na bai wa jama'a tabbacin cewa babu wata matsala da zata faru, kuma su fito su gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Imo ya ce ''akwai cikakken tsaro ga dukkan wadanda za su fito wuraren harkokinsu.'' Sai dai bai yi cikakken bayani kan irin matakan tsaro da aka tanadar ba.

Labarai masu alaka:

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto,

'Yan kabilar Igbo ne galibin mazauna kudu maso gabashin Najeriya inda IPOB ke fafutikar kafa kasar Biafra

Shin mutane za su amsa kiran 'yan a-ware ne ko kuwa na hukumomi?

Ganin yadda kungiyar a-waren ta bayar da umarni cewa kada jama'a su fito harkokinsu, a bangare guda kuma hukumomi suka bukaci jama'a su fito kamar yadda suka saba, za a iya cewa kallo ya koma sama. Shin umarnin gwamnatoci za a bi ko kuwa na kungiyar IPOB?

Wasu dai na kallon matakin na IPOB a matsayin wani yunkuri na kara jinjina karfin ikon gwamnati da kuma kara jawo hankali ga fafutikar da 'ya'yanta ke yi.

Wakilin BBC Zaharaddeen Lawan ya ce ko a karshen watan Mayu kungiyar ta IPOB ta bai wa mazauna yankin umarnin su zauna a gida, kuma a wancan lokacin mutane da dama sun bi umarnin, imma dai saboda biyayya ga kungiyar ko kuma saboda tsoron abin da zai iya faru idan suka fito.

Amma babu tabbas kan ko a wannan karon matakin 'yan a-waren zai yi tasiri wajen kassara harkoki a yankin, a cewar wakilinmu.

Shi dai jagoran kungiyar ta IPOB Nnamdi Kanu yana fuskantar tuhume-tuhume masu nasaba da cin amanar kasa, da tayar da hankali da kuma mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Hukumomin Najeriya na zargin kungiyar da kai hare-hare kan jami'an tsaro da cibiyoyinsu inda suke kashe jami'an tsaron da kona ofisoshinsu da kuma kwashe makamai. Hakan nan suna zargin kungiyar ta IPOB da kisan farar hula.

To amma kungiyar IPOB na cewa matakan da hukumomi ke dauka kan shugabanta da kuma yankin baki daya rashin adalci ne. Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ma, a wani rahoto a baya-bayan nan, ta zargi jami'an tsaron Najeriya da yin amfani da karfi fiye da kima kan 'yan awaren da ma wadanda ba su ji ba su gani ba a yankin.

A cikin watan Yuni ne aka sake kamo Nnamdi Kanu bayan da ya gudu zuwa kasar waje bayan da aka bayar da belinsa a 2017.Ana sa rana a cikin watan Oktoba ne za a ci gaba da yi masa shari'a a wata babbar kotun tarayya dake Abuja.