Mutuwar wata yarinya yayin haihuwa a coci ta harzuka mutane a Zimbabwe

Asalin hoton, UNAMID
Majalisar Dinkin Duniya ta yi tur da yi wa kananan yara aure
'Yan sanda a Zimbabwe suna gudanar da bincike game da mutuwar wata yarinya mai shekara 14 lokacin haihuwa, lamarin da ya harzuka 'yan kasar da masu kare hakkin dan adam.
Rahotanni sun ce Memory Machaya ta mutu a watan jiya a wani wurin bauta da ke birnin Marange na gabashin kasar.
Lamarin ya bayyana karara yadda ake cin zarafin kananan yara, yayin da rahotanni suke cewa an tilasta wa yarinyar barin makaranta domin ta yi aure.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnati ta ayyana auren kananan yara a matsayin laifi sannan ta kawo karshensa.
Ta bayyana lamarin da cewa "abin tayar da hankali ne" kuma ta yi tur da yadda yarinyar ta mutu da "kakkausar murya".
"Abubuwan da ke faruwa game da cin zarafin mata da kananan yara a Zimbabwe, wadanda suka hada da kananan yara da aka yi wa aure, ba za su ci gaba da faruwa ba bisa ƙeta," a cewar wata sanarwa da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ranar Asabar.
Mutuwar yarinyar ranar 15 ga watan Yuli ta jawo hankali jama'a game da yadda ake yi wa kananan yara auren wuri a cikin Cocin Apostolic da ke Zimbabwe, wadda akasari ba ta amicewa da magungunan asibiti.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Kafofin watsa labaran kasar sun ambato iyalanta suna cewa jaririyar da ta haifa tana nan cikin koshin lafiya.
'Yan sanda da hukumar kare jinsi na kasar suna gudanar da bincike game da lamarin da ya kai ga rasuwarta da kuma binne ta.
Tuni dai wasu mutane suka kaddamar da kamfe a shafukan intanet da ke kira a yi adalci game da kisanyarinyar wanda a turance suka yi wa lakabi "justice for Memory Machaya" kuma kawo yanzu fiye da mutum 57,000 sun sanya hannu kan takardar kamfe din.
Fitacciyar 'yar kasar Zimbabwe da ke kare hakkin mata Everjoice Win ta ce lokaci ya yi da za a matsa lamba kan "masu mulki su tabbatar da bin doka ko kuma su yi sababbin dokoki" kan batun.
Ta wallafa wani sako a shafinta na Tuwita da ke cewa ba a kallon manyan mata da kananan mata "a matsayin cikakkun mutane, wadanda suke da 'yanci... na yin abin da suka ga dama da jikinsu."
Dokokin Zimbabwea sun amince a aurar da yarinyar da ta kai shekaru 18, yayin da macen da ta kai shekaru 16 ana kallonta a matsayin wacce za a iya tarawa da ita.
Sai dai wasu iyayen na ganin za su rika samun kudi idan suka yi wa 'ya'yansu kanana auren wuri.