Isa Abba Adamu: Ana alhinin rasuwar tsohon shugaban Sashen Hausa na BBC

Isa Abba Adamu
Bayanan hoto,

Isa Abba Adamu ne bakar fata na farko da ya zama shugaban Sashen Hausa na BBC mai cikakken iko.

'Yan uwa da abokan aiki na ci gaba da bayyana jimaminsu na rasuwar tsohon shugaban Sashen Hausa na BBC, Malam Isa Abba Adamu.

Ya rasu ne a birnin London ranar Lahadi bayan gajeriyar rashin lafiya yana da shekaru 60 a duniya.

Fitaccen dan jaridar, wanda ya kwashe fiye da shekaru 20 yana aiki da BBC, ya bar mata daya da 'ya'ya hudu.

Ya soma aiki a BBC Hausa a matsayin mai shirya shiri inda ya rika samun ci gaba.

Shi ne bakar fata na farko da ya zama shugaban Sashen Hausa na BBC mai cikakken iko.

Kazalika, Malam Isa, ya rike mukamin shugaban Sashen Afirka na BBC.

An haifi marigayin a shekarar 1961 a birnin Kano da ke arewacin Najeriya, kuma ya kammala digirinsa na farko a Jami'ar Bayero a shekarar 1985.

Bayanan hoto,

An yi wa marigayi Isa Abba Adamu salatul ghaib a birnin Kano da ke Najeriya

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kafin ya soma aiki da BBC Hausa, ya yi aiki a Kano State Television CTV 67.

A ranar Litinin ne aka gudanar da salatul ghaib ta Isa Abba Adamu a birnin Kano da ke arewacin Najeriya.

Sai dai kafin nan, an sallace shi a birnin London.

'Aiki tuƙuru'

Malam Sulaiman Ibrahim, wani tsohon ma'aikacin BBC Hausa wanda kuma ya taba yin aiki tare da marigayi Isa Abba Adamu, ya bayyana shi a matsayin mutum mai jajircewa wurin aiki.

"Isa Abba Adamu mutum ne ma'aikaci. Yana aiki tukuru; idan yana aiki ba ka ganin ya tsaya yana wasa. Idan labarai yake yi ko kuma shirya gabatarwa, idan ka ga [Isa] ya tsaya yana labari, to ya kammala abin da zai shiga ya karanta ke nan," a cewarsa.

Ya kara da cewa abin da za a fi tunawa game da marigayi Isa Abba Adamu shi ne "yadda duk sad da ya zo tsakiyar shiri, idan ya ce 'ana sauraren Sashen Hausa na BBC ne, to sai ya ce daga tsakiyar birnin London ni kuma ni ne Isa Abba Adamu."

Latsa hoton da ke kasa domin sauraren hira da Sulaiman Ibrahim:

Bayanan sauti

Isa yana da aiki tuƙuru - Sulaiman Ibrahim