Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Messi, Lukaku, Pogba, Doku, Abraham, Lingard, Sterling

Lionell Messi

Asalin hoton, Getty Images

Watakila Manchester United ta yi kokarin shafa wa Lionel Messi zuma a baki, domin shawo kansa ya je kungiyar ya yi watsi da maganar tafiyarsa Paris St-Germain. (Jaridar Daily Star)

PSG na neman sayar da har kusan 'yan wasanta10, da suka hada da tsohon dan wasan tsakiya na Everton,kuma dan Senegal, Idrissa Gueye, mai shekara 31, domin ta kammala daukar, dan wasan na Argentina mai shekara 34. (Jaridar Athletic)

Haka kuma kungiyar ta Faransa ta kawo karshen, sha'awarta ta sayen dan wasan tsakiya na Manchester United da Faransa Paul Pogba, mai shekara 28, kila saboda kusan samun Messi a hannu. (Jaridar Le Parisien)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Samun Messi ya sa PSG ta kawo karshen neman Paul Pogba

Bayan da aka yi masa gwajin lafiya na farko na komawarsa Chelsea, dan gaban Inter Milan da Belgium, Romelu Lukaku, mai shekara 28 zai iya taka wa kungiyar wasanta na farko na Premier na bana da Crystal Palace ranar Asabar. (Jaridar Daily Star)

Lyon ta gabatar da bukatarta ta sayen dan wasan gaba na Liverpool da Switzerland Xherdan Shaqiri, mai shekara 29. (Jaridar L'Equipe)

Manchester United za ta tabbatar da kammala sayen dan bayan Real Madrid Raphael Varane, mai shekara 28, ranar Larabar nan, domin ta samu damar amfani da shi a wasanta na Premier na ranar Asabar da Leeds. (Jaridar Daily Star)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasa 79 Varane ya buga wa Faransa inda ya fara a 2013

Liverpool na duba yuwuwar sayen matashin dan wasan gaba na gefe na kungiyar Rennes, dan Belgium Jeremy Doku, mai shekara 19. (Daga Voetbal 24)

Dan wasan gaba na Chelsea, kuma dan Ingila Tammy Abraham, mai shekara 23, na daukar hankalin Arsenal da Roma da kuma Atalanta. (Daga Goal)

Kociyan Roma Jose Mourinho na sha'awar sayen dan gaban Arsenal kuma dan Faransa Alexander Lacazette, mai shekara 30. (Daga Gazzetta dello Sport)

Leicester na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Manchester United Jesse Lingard, mai shekara 28, idan hard an uwansa dan Ingila James Maddison,mai shekara 24, ya bar kungiyar. (Jaridar Football London)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jesse Lingard ya yi zaman aro ne a karshen kakar da ta gabata a West Ham

Haka kuma an ce Leicester din na son dan bayan Schalke, dan Turkiyya Ozan Kabak, mai shekara 21 - wanda ya yi zaman aro a Liverpool a karshen kakar da ta gabata, Foxes na kuma son dan bayan West Ham, dan Faransa Issa Diop, mai shekara 24. (Jaridar Leicester Mercury)

Everton na sha'awar dan wasan tsakiya na Newcastle United, dan Ingila Sean Longstaff, mai shekara 23. (Jaridar Athletic)

Bayern Munich na tunanin sake daukar Franck Ribery. Dan wasan gaban na gefe, dan Faransa, mai shekara 38 na atisaye da kungiyar tun da ya bar Fiorentina. (Gazzetta dello Sport)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Franck Ribery ya tafi Fiorentina bayan karewar kwantiraginsa da Bayern bayan shekara 12 a Bundesliga

Dan wasan gaba na gefe na Manchester City, dan Ingila Raheem Sterling, mai shekara 26, na shirin tattaunawa kan sabon kwantiraginsa da kungiyar. (Sun)

Dan wasan tsakiya na Tottenham, dan Faransa Tanguy Ndombele, mai shekara 24, na tunani kan ci gaba da zamansa a kungiyar ta arewacin London. (Athletic)