Petroleum Industry Bill: Abin da ya sa muke goyon bayan dokar man fetur - Kyari

PIB

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An shafe shekara ana ce-ce-ku0ce a kan ƙudurin dokar man fetur

Masu ruwa da tsaki a harkokin da suka shafi man fetur da gas a Najeriya na ci gaba nuna gamsuwa da matakin da shugaban kasar ya dauka na sanya hannu kan dokar inganta harkar mai, wato PIB.

A ranar Litinin 16 ga watan Agusta ne Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba wa dokar hannu bayan da majalisun dokokin kasar suka amince da ita a watan jiya.

An shafe fiye da shekara 20 ana ce-ce-ku-ce a kan dokar.

Sai dai duk da sukar dokar da wasu ƴan ƙasar ke yi, Shugaban Kamfanin Mai na Najeriyar NNPC Alhaji Mele Kyari ya kare dokar da cewa tana da matuƙar muhimmanci.

Gagarumar nasara

Alhaji Mele Kyari ya ce sanya hannun da shugaban ƙasa ya yi kan dokar gagarumar nasara ce ga Najeriya da kuma masana'antar man fetur baki ɗaya.

"Sanin kowa ne an fi shekara 20 ana fama a kan dokar nan. Duk ƙudurorin da suke cikin ayyukanmu da muke yi kame-kame ne tun shekara 1967, na dokar Petroleum Act da aka samar.

Ya koka cewa kusan shekara 50 kenan ba a samu wani sauyi a kan irin ayyukan da ake yi a ɓangaren man fetur ba.

"Duniya ta ci gaba irin ayyukan da muke yi duk an sauya yadda ake gudanar da su, amma mu mun gagara yi tsawon shekara da shekaru.

"A misali kamfanoni sun zuba jari a Afirka na dala biliyan 50, amma a ciki uku ne kawai suka shigo Najeriya cikin shekara 10 da suka gabata.

"Kuma ba komai ya jawo hakan ba sai kasancewar dokokinmu ba irin na zamani ba ne, saboda ba su da tabbas din yadda kudinsu zai fito idan suka zuba jarin, da sauran abubuwa da dama," a cewarsa

Kyari ya ce zamani ya wuce ya bar Najeriya a baya a fannin man fetur, "dole sai mun gyara, shi ya sa muka jajirce."

Shugaban kamfanin na NNPC ya ci gaba da cewa "Don haka gaskiya wannan gagarumar dama ce a gare mu musamman da za mu samu kwararowar masu zuba jari cikin ƙasar.

"A kwanakin baya manyan kamfanonin irin su Shell da Chevron har barazanar janyewa su bar ƙasar suka yi.," ya ƙara da cewa.

Asalin hoton, NNPC

Bayanan hoto,

Talaka ne zai fi cin ribar wannan sauyi, in ji Mele Kyari

Me ya sa aka shafe shekaru ba a yarda da dokar ba?

Kyari ya ce dama an sani a duniya masana'natar man fetur rigimammiya ce, shi ya sa kullum idan aka tashi gyara sai ya gagara.

"Na farko ba a samu cikakkiyar alaƙa tsakanin majalisun dokoki da gwamnatin tarayya ba tsawon shekara 20 ɗin nan.

"A lokutan baya an yi ta ƙorafin a gyara dokar amma sai ka ga ko dai shugaban ƙasa na lokacin ya ƙi ko kuma ƴan majalisa su ƙi.

"Bambancin da aka samu a yanzu shi ne akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin ƴan majalisar dokoki da ɓangaren gwamnatin tarayya da ɓangaren zartarwa.

"Wannan ne ya sa aka cimma nasara wajen kawo ƙarshen wannan tataɓurzar," a cewarsa.

Kazalika ya ce an samu dama ta tattaunawa da manyan kamfanonin da abin ya shafa.

Wane sauyi dokar za ta kawo ga harkokin man fetur a Najeriya?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mista Kyari ya ce dokar za ta sauya abuuwan masu yawa a ƙasar.

1. Na farko za a samu zuba jari sosai a bangaren man fetur.

"A da ba a tantance abubuwan da idan mutane sun zuba jari kudinsu zai fito.

2. Akwai wurare da yawa a aduniya da suke da mai wadanda dokokinsu ke da kyau, da idan ba a gyara namu ba za su dinga tafiya can suna barinmu," in ji shugaban NNPC.

3. Na uku rashin tabbas din da ake da shi a kasar ya sa kamfanonin sun daina zuba jari.

Wannan doka za ta kawo ɗorewar zaman masu sa jari kuma zai ba da dama a mai da hankali kan ayyukan iskar gas da a baya ba a mai da hankali a kansa.

Shi kuwa gyaran bangaren iskar gas zai kawo wa kasa arziki da gyara yanayi, kamar yadda ya ce.

4. Na hudu shugaban kamfanin man ya ce dokar za ta gyara batun yadda ake samar da man fetur a kasa da yadda ake amfani da shi.

"Da can ba a yi saboda akwai dokokin da suke hana ruwa gudu saboda gudun sauyin matakan gwamnati na rashin tabbas.

"Za a samu yanayi mai kyau na sarrafa danyen man fetur a gida don amfaninmu."

Ta yaya dokar za ta amfani talaka?

Wasu da dama na ganin cewa dokar masu kudi da ƴan boko kawai za ta yi wa amfani ban da talaka.

Sai dai Mista Kyari ya musanta hakan, inda ya ce "ai duk bayanan da na yi a sama ma za su amfani talaka.

"Misali idan masu zuba jari suka shigo ƙasar aka samar da masana'antu ai za a samu ayyukan yi sosai. Sannan gwamnati za ta samu dukiya ta yi wa mutane aiki

"Da zarar dokar nan ta dore za a ga ayyuka sun samu, jarin ƴan kasuwa ya bunƙasa, bankuna za su shigo ƙasar sannan za a samu damar wadata ƙasar da iskar gas da wutar lantarki.

"Talaka ne zai fi cin ribar wannan sauyi," in ji Mista Kyari.