Muhammadu Sanusi na II: Gwamnatin Kaduna na shan suka kan shirya taron murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Masu sukar na cewa bai kamata a kashe kudin jama'ar Kaduna alhalin suna cikin tsaka mai wuya ba

Asalin hoton, @NASIRELRUFA'I

Bayanan hoto,

Masu sukar na cewa bai kamata a kashe kudin jama'ar Kaduna alhalin suna cikin tsaka mai wuya ba

Ana ci gaba da cacar baki tsakanin bangaren 'yan adawa da na gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya, dangane da daukar dawainiyar walimar cika shekaru 60 na tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II. 

Hatta a shafukan sada zumunta wasu 'yan jihar na ce-ce-ku-ce a kan gudunmuwar da ake zargin gwamnatin jihar ta bayar ta Naira miliyan 25 wajen gudunar da taron sarkin, wanda amini ne ga gwamnan Kaduna Nasir Ahmad el-Rufai.

'Yan jam'iyar adawa ta PDP a jihar na cewa an yi facaka da makudan kudade wajen shagali, yayin da talakawa musamman ma'aikata ke cikin halin kuncin rayuwa.

Mohammad Dan Auta, na Jam'iyar hamayya ta PDP, na cikin masu sukar lamarin kuma yana da ra'ayin cewa babu wani dalili da zai sa gwamnati kashe wannan kudi domin kawai ''Shirya bikin taya abokin gwamna murnar zagayowar ranar haihuwarsa''.

''Shi kansa Sarki Sanusi ya yi godiya ga gwamnatin Kaduna kan daukar nauyin wannan taro, sannan ga takarda mai dauke da sa hannun mataimakiyar gwamna da ke bayar da umarnin fitar da wannan kudi, don haka ya kamata gwamnati ta daina kashe kudaden jama'a wajen shirya sharholiya''

Asalin hoton, @NASIRELRUFA'I

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin mahalarta taron da aka gudanar a Kaduna

Sai dai wasu mukarraban gwamnan jihar sun ce ba lallai ne ikirarin da masu sukar ke yi ya kasance gaskiya ba, hasali ma dai ko da hakan ya tabbata, tamkar ai yi wa kai ne.

Mohammad Lawal Shehu, wato Molash, mataimaki na musamman ne kan harkokin siyasa a shiyya ta daya ga gwamnan jihar Kaduna, ya ce idan ma zargin ya tabbata, ba laifi ba ne don an yi hakan ga Sarki Sanusi, domin irin rawar da yake takawa wajen ciyar da jihar gaba.

''Mai girma Muhammadu Sanusi II shine shugaban jami'ar jihar Kaduna, shi ne mataimakin hukumar saka hannun jari ta Kaduna, sannan yakan janyo Turawa domin su zo su zuba jari a Kaduna."

Ya musanta cewa an ki biyan ma'aikata albashinsu yayin da aka shirya wannan taro, inda ya ce duk ma'aikacin da ba a biya hakkinsa ba to watakila yana da matsala ne da ma'aikatar kudi ta jihar, saboda tantance ma'aikata da aka yi a baya bayan nan.

Matashiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An gabatar da jawabai kan rayuwar tsohon sarkin na Kano na 14

A ranar Asabar ne aka gudanar da taron gabatar da makaloli na shekara-shekara kan cikar tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II shekara 60 a duniya.

An gudanar da taron ne a dakin taro Umaru Musa 'Yar Adua da ke birnin Kaduna a jihar ta Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.

Taron shi ne irinsa na farko kuma ana sa ran za a ringa gudanar da shi a kowace shekara.

A wajen taron, masana sun gabatar da makaloli kan irin sauye-sauyen da Sarki Sanusi ya kawo a wuraren da ya samu damar yin aiki.